For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JAMB Zata Yanke Makin Shiga Makarantu A Watan July Mai Kamawa

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB ta shirya gudanar da zaman tattaunawa na shekarar 2022 kan tsare-tsarenta game da shekarar karatu ta 2022/2023 a ranar 21 ga watan Yuli mai kamawa.

Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin ne ya baiyana hakan a saƙon kar-ta-kwana da ya aikewa wakilin PUNCH a Abuja.

Zaman fitar da tsare-tsaren dai, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne zai jagoranta inda dukkanin shugabannin manyan makarantu zasu halarta.

Zaman tattaunawar dai zai mai da hankali kan hanyoyin bi ga manyan makarantun Najeriya, ya fitar da ƙa’idojin shiga makarantu, sannan ya yi duba na tsanaki kan buƙatun shiga makarantu da ake da su, da kuma duba yanayin ɗaukar dalibai a makarantun.

Mutanen da basu gaza 1,761,338 ne ba suka yi rijistar zana jarabawar JAMB da kuma cike DE a shekarar nan ta 2022.

Hukumar ta ce, mutane 1,707,626 ne suka sami damar rubuta jarabawar, yayin da sakamakon mutane 1,671,203 ya fito.

Kididdigar tai ta nuna cewa, akwai sakamakon mutane 27,105 wanda ake kara tantancewa.

Haka kuma, hukumar ta ce ta rike sakamakon mutane 69 yayin da kuma take shirin sanyawa wadanda suka sami matsalar daukar hoton yatsunsu su 1,783 wani lokacin na rubuta jarabawar.

Comments
Loading...