Rundunar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nigeria reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kubutar mutane 20 wadanda akai yunkurin safararsu a samamenta da dama a shekarar 2021.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, ASI Nura Usman ne ya bayyana hakan lokacin da yake magana da Kamfanin Dillancin Labari na Nigeria, NAN yau Alhamis a Dutse.
ASI Nura ya bayyana cewa an kubutar da mutanen ne a tsakanin watannin Mayu da Satumba na shekarar 2021.
Ya yi bayanin cewa 7 daga cikin wadanda aka so yin fataucinsu an kubutar da su ne a ranar 7 ga Mayu, 4 kuma a ranar 17 ga Mayun, yayinda aka kubutar da guda 9 a ranar 6 ga watan Satumba.
KU KARANTA: ‘Yansanda A Zamfara Sun Kama Masu Ci Da Siyar Da Naman Mutane
Jami’in Hulda da Jama’ar ya kara da cewa, an kuma samu nasarar kama daya daga cikin masu safarar mutanen a lokacin samamen.
“Dukkan wadanda akai kokarin safarar ta su, an mika su ga Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa, NAPTIP.
“An kubutar da mutanen ne a lokacin da ake kan hanyar kai su birnin Tripoli na kasar Libya ta cikin Jamhuriyar Niger.
“Wadanda akai safarar da su, shekarunsu na tsakanin 16 da 33 ne, kuma sun fito daga jihohin Benue, Ekiti, Lagos, Ogun, Oyo, Kwara da Imo,” in ji shi.
ASI Nura ya bukaci al’umma, musamman iyaye da su guji fadawa yaudarar masu yi musu romon baka kan kyakkyawar rayuwa a kasashen waje.
Ya kuma bukaci al’umma da a ko da yaushe su dinga fallasa abubuwan da suka shafi safarar mutane da sauran laifuffuka ga hukumomi.