A kalla mutane 11 ne suka sami raunuka a fashewar gas din da ta faru a Karamar Hukumar Babura da ke Jihar Jigawa.
Al’amarin dai ya faru ne a daren Litinin a garin Gwamnan Jihar, Badaru Abubakar, bayan jami’an Kwastom sun biyo motar da ke dauke da tukwanen gas.
DSP Lawal Shiisu, wanda shine Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ba a rasa rai ba a dalilin lamarin.
Ya ce, wadanda suka sami raunuka daban-daban a dalilin hatsarin an kai su Babban Asibitin Babura domin a yi musu magani.
“Wasu daga cikin jami’an kwastom da ke aiki a bakin boda, sun biyo mota kirar IVECO wadda ke dauke da tukwanen gas daga Kasar Nijar da nufin zuwa Karamar Hukumar Gumel da ke jihar,” in shi.
“Daya daga cikin tunkuyar gas din ta fado ta kama da wuta lokacin tana kan titi a Babura, sai kuma fashewar ta fara.”
Da yake bayar da bayani kan yanda al’amarin ya faru, wani mazaunin garin Babura, Mujahid Aliyu ya ce, lamarin ya faru ne a kusa da gidansa.
Ya zargi jami’an tsaro da haddasa lamarin inda ya ce, matsalar fashewar ta jawo gagarumar asara a gidansa da motarsa.
“Wasu jami’an kwastom sun biyo mota mai dauke da tukwanen gas sannan suka yi harbi a kan motar sau biyu ko sau uku. Hakan ce ta sa fashewar ta fara,” in ji Mujahid.
Wani mazaunin garin na Babura, Dauda Rabi’u ya ce, da farko ya yi tunanin harbi ne, amma daga bisani ya gano cewa fashewa ce.
“Mun yi tunanin harbin bindiga ne, saboda mun saba da jin harbe-harben bindigar kwastom a kullum. Amma daga baya na gano cewa abun ya fi karfin haka, sai na fara kokarin ceton ‘ya’yana da naga fashewar na ta ci gaba,” in ji shi.