Jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri da aiki a iyakar Seme, sun kama wasu abubuwa da ake zargin kwayoyin tramadol ne a cikin kunshin kunzugun maza da suka kai 200.
Jami’in Hulda da Jama’a na reshen hukumar, Hussaini Abdullahi, ya ce abubuwan laifin da aka kawo a kwantena mai girman 1X20 an biya musu harajin da ya kai Naira Biliyan 1.45.
Kwantenar mai lambar rijista MRKU 9090415, an mika ta ga reshen hukumar a ranar 15 ga Nuwamban 2021 daga hukumomin kasar Benin.
KU KARANTA:
- Kungiyar CAN Ta Yi Barazanar Daukar Mataki Idan A Kai ‘Yan Takara Musulmi A Najeriya
- Wani Sojan Gona Ya Damfari Mutane Tare Da Yaudarar Mata Yana Lalata Da Su
Hussaini ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kawo kwantena jami’an suka sanya ma ta idanu, kuma ba a samu wani wanda ya shigo da ita ko wakilinsa ba da ya zo domin bukatarta, hakan ne ya sa ake zargin kwantenar.
Wannan zargi shi jawo akai bincike a kan ta, wanda aka sami hadin guiwar wasu jami’an tsaron bayan Kwantirolan Sashin, B.M Jibo ya bukaci ai hakan.
Bayan binciken an gano kunshi-kunshin kunzugun maza har guda 200, katan-katan na Gabadol mai nauyin 120mg, wadanda ake zargin kwayoyin tramadol ne, wanda yai daidai da nauyin kilogram 360 a karshen binciken.
Ya bayyana cewa, an jera kunzugun mazan sosai a gaban kwantenar, yayin da ka boye kwayoyin daga baya.