For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jami’an Tsaro Sun Ceto Malaman Jami’ar Abuja

Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja hadin guiwa da sauran jami’an tsaro, ta ceto malaman nan hudu da iyalansu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su da safiyar ranar Talata a gidanjensu na jami’ar Abuja.

Jami’in Kula Da Al’amuran Dalibai na jami’ar ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “wadanda aka sace a UniAbuja an ceto su, ba a samu rauni ba, ba a biya kudin fansa ba. An kama mutane da yawa masu hannu Alhamdulillahi!!!”

Josephine Adeh, Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayyar ta tabbatar da batun a wani jawabi yau da safe.

“Hukumar ‘Yan Sandan FCT na farincikin sanar da al’umma cewa duk wadanda akai garkuwa da su a Jami’ar Abuja an kubuto da su kuma sun koma cikin iyalansu, aikin da aka gudanar hadin guiwa da sauran jami’an tsaro. Sauran bayanai game da lamarin na nan tafe.”

In za a iya tunawa dai masu garkuwa da malaman sun bukaci a ba su Naira Miliyan 300 a matsayin kudin fansa bayan kwana daya da kama malaman.

Comments
Loading...