For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Da Wasu Ƴan Ta’adda 27 A Borno

Jami’an Tsaro na rundunar Sojan Sama masu taken Operation Hadin Kai sun kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram mai suna Alhaji Modu wanda aka fi sani da Bem Bem.

Haka kuma jami’an sun samu nasarar kashe wasu ƴan ƙungiyar ta Boko Haram har su 27 duk a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas ɗin Najeriya.

Sanannen kwamandan na Boko Haram da abokan aikinsa, an kashe su ne a ranar 3 ga watan Agustan nan da muke ciki ta hanyar jefa musu abun fashewa ta sama a yankin tsaunukan Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Majiyoyi daga ɓangaren sojoji sun tabbatar da cewa an kai harin yanda ya kamata bayan samun bayanan sirri na nuni da cewa, ƴan ta’addar ƙungiyar ISWAP na taruwa a wajen domin kaiwa harin ta’addanci.

Mataccen mayaƙin Boko Haram ɗin, Alhaji Modu sanannen ɗan harkar ƙwaya ne wanda ya shiga harkar fashi da makami kafin daga bisani ya shiga ƙungiyar Boko Haram.

Majiyoyi sun bayyana cewa, Bem Bem shine ya jagoranci ƙwace garin Bama a shekarar 2014 tare da kashe ɗaruruwan mutane kafin daga bisani ya bayyana ta a matsayin shelkwatar daular Boko Haram.

Kafin mutuwarsa, Bem Bem na yin aiki ne ƙarƙashin kulawar babban jagoran ƙungiyar Boko Haram, Ali Ngoshe kuma suna ɓoyene a cikin kogo a kan tsaunukan Mandara inda suke shirya kai hare-hare Najeriya, Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Rundunar Sojojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya buƙaci kwamandojin sojojin da kar su nuna tausayawa tare da tabbatar da sun yi amfani da duk wani ƙarfi a kan ƴan ta’addar da suka addabi tsaron kasar nan.

Comments
Loading...