For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Makamai

Runduna ta 4 ta Sojojin Najeriya da ke aiki na musamman kan bayanan sirri ta samu nasara a kan masu garkuwa da mutane guda uku, wadanda ake zargi da hana zaman lafiya a kan sanannen titin nan na Auchi zuwa Benin da ke jihar Edo.

Masu garkuwa da mutanen sun gamu da gamonsu ne a ranar Laraba a lokacin da suke aika-aikarsu a yankin.

An samu nasarar ne lokacin da sojojin suka far musu, abin da ya jawo musayar harbe-harben da sukai sanadiyyar kashe uku daga cikin gungun masu garkuwa da mutanen, yayinda sauran suka tsere.

KU KARANTA: Kar Ku Bar ISWAP Ta Girma – Zulum Ga Gwamnatin Tarayya

Mai Magana da yawun Sojoji, General Onyema Nwachukwu, ya baiyana cewa, sojojin sun samu nasarar kwato gindin harsasan bindiga kirar AK 47, karamar bindiga guda daya da kuma sauran muggan makamai.

Haka kuma, ana cigaba da bibiyar batagarin da suka tsere da kuma yunkurin tabbatar da toshe duk wata kofa da suke samu wajen tayar da hankalin mutane, haka kuma mai magana da yawun sojojin ya yi kira ga mutane musamman al’ummar jihar Edo da su cigaba da tona asirin batagarin.

An kuma shwarce su da su cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba tare da tsoro ba, inda aka tabbatar musu da yin duk mai yiwuwa wajen samar da zaman lafiya.

Wasu daga Cikin Makaman da aka kwata
Comments
Loading...