Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 10 a kusa da garin Fatika da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Haka kuma rahotannin da BBC ta samu sun nuna cewa wasu maharan sun jikkata a yayin musayar wuta da jami’an tsaron.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da aka yi garkuwa da shi.
Aruwan ya kara da cewa ‘yan bindigar da suka sami tserewa sun bar baburan su da wata babbar bindiga da wayoyi da fitilu da kuma layu.
Ya kuma ce an kona wasu daga cikin wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.