Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta fitar da sanarwar kara yawan kwanakin hutun dalibai a zamanta na 392 wanda aka gudanar ranar Larabar da ta gabata.
A cewar Malam Jamil Ahmad Salim, Mai Rikon Kujerar Rijistaran Jami’ar, an yanke hukuncin kara tsayin hutun ne saboda a baiwa masu son shiga jami’ar dama musamman wadanda jarabawarsu ta kammala Sikandire ba ta fito ba.
Sanarwar ta ce “Tun da ya tabbata cewa Jarabawar NECO ba za ta fito bas ai a farkon watan Oktoba, ga kuma burin da muke da shi na baiwa dalibai damar shigowa jami’armu, Hukumar Gudarwar Jami’ar ta yanke shawarar kara kwanakin hutu da wata guda.”
A yanzu dai dalibai za su koma jami’ar ne a ranar 1 ga Nuwamba don fara karatun shekarar 2021/2022, sannan za a fara darussa ranar 8 ga watan.
Hukumar Jami’ar ta lura cewa kashi 90% na daliban da suka cancanci samun adimishin ta hanyar cin maki 180 a JAMB suna dakon sakamakon jarabawar kammala sikandire.