For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jamíyyar APC Na Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

Jam’iyyar APC ta fara gudanar da tantancewa ga masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben shekarar 2023.

Ana gudanar da tantancewar ne a Transcorps Hilton Hotel a Abuja.

Tun a farko dai an sanya ranar 23 ga watan Mayun nan, amma daga baya shugabancin jam’iyyar ya dage tantancewar ba tare da sanya sabuwar rana ba.

Sai dai kuma ba a yarjewa ‘yan jarida shiga Transcorps Hilton, wajen da ake gudanar da tantancewar ba.

Wakilin DAILY TRUST ya rawaito cewa, tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne na farko da aka tantance.

Sai dai Nwajiuba ya ki yi wa manema labarai bayani bayan ya sakko daga wajen da ake tantancewar.

Sauran wadanda ake sa ran za a tantance dai sune: Jagoran APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; tsohon Ministan Ma’aikatar Harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio; Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; tsohon Gwaman Jihar Ogun, Ibikunle Amosun; Gwamnan Jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi; tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha.

Sauran sune: Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan; Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi; Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar; Pastor Tunde Bakare; Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Ken Nnamani; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon Gwamnan Zamfara, Sani Yarima; tsohon Ministan Yada Labarai, Ikeobasi Mokelu da ‘yar takara mace guda daya Uju Ohanenye; Nicholas Felix; tsohon Kakakin Majalissar Wakilai, Dimeji Bankole; Tein Jack-Rich da sauransu.

Comments
Loading...