For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jam’iyyar APC Ta Dage Ranar Babban Taronta Na Kasa Zuwa 26 Ga Maris

Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC wanda aka nada shi domin gudanar da Zaben Shugabannin Jam’iyyar na Kasa, ya mika kai bori ya hau, ya kara canza ranar gudanar da Babban Taron Jam’iyyar na Kasa wanda da aka shirya gabatarwa ranar 26 ga watan nan na Fabrairu zuwa ranar 26 ga watan Maris mai zuwa.

Wannan mataki ya biyo bayan zaman tattaunawa na 20 wanda kwamitin rikon ya gabatar jiya Litinin a Abuja.

Da yake yiwa manema labarai karin haske jim kadan bayan kammala zaman tattaunawar da ya debe kimanin awanni uku, Sakataren Riko na Jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanuadoedehe ya ce, “Mun amince kuma yarda da tsare-tsaren gudanar da Babban Taron Jam’iyya na Kasa su fara gudana ranar 24 ga watan Fabrairu su kuma kare a ranar 26 ga watan Maris da zabar shugabannin jam’iyya a matakin kasa wanda za a gudanar a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

“A tsakanin shirye-shiryen babban taron, mun amince da gudanar da manyan tarurrukan shiyya-shiyya, haka kuma kwamitin rikon ya yarje da duk tsare-tsaren.

Jadawalin tsare-tsaren da sakataren rikon ya bayar ga manema labarai ya nuna cewa, duba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar a Article 12.6, za a gudanar da tarurrukan shiyya-shiyyar ne ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2022.

Kwamitin Rikon APC wanda Mai Mala Buni yake jagoranta an kafa shi ne a ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 2020 domin ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar cikin watanni 6 bayan rushe shugabannin da Adams Oshiomole ya jagoranta.

Comments
Loading...