Jaridar JakadiyaPress ta sami tattaunawa da matashin dan siyasa daga jam’iyyar PDP a jihar Jigawa, Haruna Shuaibu Danzomo a kan Babban Zaben da Jam’iyyar PDP ta gabatar ranakun Asabar 30 da Lahadi 31 ga watan Oktoba, 2021.
Ga yanda hirar ta kasance:
Jakadiya: Ya ka kalli Babban Zaben Jam’iyyar PDP na kasa?
Danzomo: Idan kace zabe sai ince kamar baka fahimci abin da ya faru ba a wajan, ai taro ya kamata ka tambaye ni, amma tunda kace zabe sai ince alhamdulillah kaso 99.5 na kujerun sasanto aka yi.
Jakadiya: Sasanto ai shima zaben ne irin wanda jam’iyyarku ta PDP ta yarda da shi tun a baya.
Danzomo: Hakane ita jam’iyyar PDP akan sasanto ta dogara, sai dai idan ba’a samu hakan ba. Don haka alhamdulillah duk yadda mutum ya dauki abin ya yi kyau kuma ya yi daidai tunda an yi lafiya an kammala lafiya babu mai korafi.
Jakadiya: Ina kake ganin jam’iyyar PDP ta dosa a Najeriya, duba da sakamakon wannan babban taro?
Danzomo: Alhamdulillah, akwai alamun cewa jam’iyyar PDP ta hau hanyar karbar gwamnati daga jam’iyyar APC tunda ai na fada maka sasanto aka yi wanda kuma yana daga cikin alamun hadin kai, hadin kai kuma a jam’iyya babbar alama ce ta nasarar jam’iyya a duk inda take. Domin akwai masu ganin cewa ba za’a gama taron lafiya ba ma.
Ammafa wannan ga kasa ne kadai babu mamaki a wasu Jihohin ka samu akwai rikici, duba da cewa yanzu haka ba ai Babban Taron Arewa maso Yammacin Nigeria ba na Jam’iyyar saboda rikice-rikice. Amma dai ba zai shafi inganci ko sakamakon zabukan na kasa ba.
Jakadiya: Ya kake ganin sabon shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu, wajen iya magance matsalolin da ake samu nan da can na rarrabuwa a wasu jihohin da ma yankuna?
Danzomo: Kasan ana cewa ba’a yabo a siyasa sai mutum ya yi an gani. Amma dai duba da tarihin sa na siyasa zamu iya cewa muna masa kyakkyawan zato, duba da cewa shi dattijo ne kuma yana da kishin jam’iyyar saboda yana daga cikin mutane 9 da suka fara yin jam’iyyar baki daya ma, don haka muna masa fatan ya fidda mana kitse daga wuta kuma ya kare mutuntakar sa da mutane suke gani.
Jakadiya: Akwai alkawari da yai na yin duk me yiwuwa wajen ganin wadansu da suka bar jam’iyyar saboda an bata musu za su dawo, kana ganin hakan me yiwuwa ne?
Danzomo: Kwarai kuwa zai iya idan har ya bi hanyar da zai tabbatar da kyakkyawan zaton da ake masa kamar yadda na fada a baya.
Jakadiya: Akwai rade-radin cewa gwamnonin jam’iyyarku ne suka daure masa gindi har ya zama shugaban domin ya biya musu bukatarsu. Kana ganin kuwa hakan abu ne da zai zamewa jam’iyyar da mai ido?
Danzomo: Rade-radi kace ko? To wasu ma suna rade-radin cewa Maigirma Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alh. Atiku Abubakar ne ya daure masa gindi. Ka ga ai du rade-radi ne, sannan tunda akayi sasanto ai ina ga babu batun cewa wani ko wasu ne suka kawo shi. Yanzu ya zama na kowa kenan.
Jakadiya: A shekarar 2018 lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar, an yi zargin cewa kudadene suka taka rawa wajen fitar da gwanayen ba duba cancanta ba, kuma hakan na daga cikin dalilan da ake zargin sun kai jam’iyyar ga rasa nasara a zaben 2019. Kana ganin sabon shugaban zai iya kawo canji ga irin wannan al’ada idan har ka yarda akwai ta?
Danzomo: Bari kaji yanzu fa jam’iyyar APC ta ganawa mutane azaba don haka babu mai kara zabarta kaji, ko don haka batun zaben fidda gwani a bari mu ga lokacin. Kuma ai babu mamaki ma kato bayan kato za’a yi zaben ka ga ai talakawa sai suyi hukunci ko?
Jakadiya: Amma batun anfani da kudin nan wajen siyan masu zabe fa, abu ne da yake rusa tsarin demokaradiya. Kuma jam’iyyarku ta yi kaurin suna kan haka. Kana ganin sabon shugaban zai iya kawo gyara a kan hakan?
Danzomo: To yanzu wacce jam’iyyar ce ba ta amfani da kudi? Kuma ba ma a zaben fidda gwani ba har babban zaben ma, don haka ai duk zargi ne kuma ka ga ai babu tabbas. Idan kuma hakane muna fatan Allah ya ba shi ikon kawo canji.
Jakadiya: Kana ganin sabon shugaban na da karfin iya shugabantar kowa a jam’iyyar ko da kuwa jam’iyyar ta karbi shugabncin kasa a 2023?
Danzomo: Ya ishi kowa amsa tunda sasanto ne ya kawo shi ba zabe ba. Ka ga ai kowa ya yadda da shi kenan.