For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jam’iyyar APC Ta Sake Sauya Lokutan Zaɓuɓɓukan Fidda Gwanayenta

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya har yanzu dai ta sake yiwa jadawalin gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwanayenta kwaskwarima.

Zaɓuɓɓukan da sauyin ya shafa sune, zaɓuɓɓukan fidda gwanaye na gwamnoni, ƴan Majalissun Jihohi, ƴan Majalissar Wakilai da kuma na Majalissar Dattawa.

Waɗannan sauye-sauyen sun zo ne kwana ɗaya bayan Kwamitin Shugabancin Jam’iyyar APC na Ƙasa ya sanar da ɗage aikin tantance masu neman takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Felix Morka ne ya sanar da sauye-sauyen a daren jiya Litinin a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.

Felix Morka ya ce, masu neman takarar gwamna guda 145 da aka tantance da masu neman takarar zama ƴan Majalissun Jihohi (su kimanin 3000) za su gwada ƙwanjinsu ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu na 2022.

A sanarwar da TASKAR YANCI ta samu, Sakataren APC na Ƙasa ya ce, “Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Ƙasa, (NWC) na Jam’iyyar APC, a ranar Litinin 23 ga watan Mayu, 2022, ya amince da sauye-sauye a Jadawalin Gudanar da Zaɓuɓɓukan Fidda Gwanaye ɓangaren masu neman takarar gwamna, ƴan Majalissun Jihohi, ƴan Majalissar Dattawa da ƴan Majalissar Wakilai kamar haka:

“Ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu, 2022 – Zaɓen Fidda Gwanaye na Masu Son Zama Gwamnoni.

(A dai ranar ta Alhamis akwai kuma), Zaɓen Fidda Gwanaye na Masu Son Zama Ƴan Majalissun Jihohi.

“Ranar Juma’a, 27 ga watan Mayu, 2022 – Zaɓen Fidda Gwanaye na Masu Son Zama Ƴan Majalisar Dattawa.

“Ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, 2022 – Zaɓen Fidda Gwanaye na Masu Son Zama Ƴan Majalissar Wakilai.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A lura cewa, akwai Babban Taro domin Zaɓen Fidda Gwani na Masu Son Zama Shugaban Ƙasa a tutar jam’iyyar, wanda za a gudanar kamar yanda aka tsara a baya, a ranakun Lahadi 29 da Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.

Comments
Loading...