Daga: Haruna Ahmad Bultuwa
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya bayyana ranar 26 ga watan Fabarairu a matsayin ranar gudanar da Babban Taron Jam’iyyar APC.
Mai Mala Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya bayyana haka ne a ranar Talata a wurin taron mata masu cigaba na kasa na shekarar 2022 da aka yi a cibiyar taron kasa da kasa, ICC, da ke Abuja.
Ya ce jam’iyyar tana dogaro da goyon bayan mata don gudanar da Babban Taron cikin nasara.