Jam’iyyar All Progressives Congress APC ta yi watsi da wasikar da hukumar zabe ta kasa INEC ta aike mata na cewa tana bukatar a sanar da kwanaki 21 akalla kafin taron gangamin da aka shirya ranar 26 ga Mairs, 2022.
Shugaban matasan APC kuma kakakin kwamitin rikon kwarya, Barista Ismail Ahmed, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja.
Yace jam’iyyar tuni ta sanar da hukumar niyyar taron gangaminta na ranar 26 ga Febrairu kuma abinda ake bukata yanzu shine fadawa INEC ta dage taron amma ba sabon sanarwa ba.
(LEGIT HAUSA)