Shugabancin Jam’iyyar National Rescue Movement, NRM, reshen Jihar Bayelsa ya baiyana cewa, a yanzu haka babu jam’iyyar a jihar.
Sun baiyana cewa jam’iyyar ta narke zuwa jam’iyya mai mulkin jihar, Peoples Democratic Party, PDP.
Wannan sanarwar ta baiyana ne a yau Alhamis daga Shugaban Jam’iyyar Mr. Kenny K. Amgbare, wanda ya jagoranci sauran shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zuwa ofishin mai baiwa Gwamnan Bayelsa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa a Yenagoa.
Amgbare ya baiyana cigaban da jagorancin Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya kawo a matsayin wasu daga cikin dalilan da ya jawo hukuncinsu na shiga jam’iyyar PDP.
Da yake karbarsu a jam’iyyar PDP, Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa, Collins Cocodia, wanda yake tare da Mai Baiwa Shawara Kan Harkokin Alaka da Jam’iyyu, Suokiri Jackson, matakin da masu shiga jam’iyyar suka dauka ya yi dai-dai.
Cocodia ya ce kofar Gwamna Diri a bude take, inda ya kara da cewa, tsarin ciyar da Bayelsa gaba ya kamata ya cigaba, “saboda mu ‘yan Bayelsa ne da farko kafin maganar jam’iyyu, saboda haka akwai bukatar kowa ya zo a goyawa gwamna mai abun mamakin baya.”
Ya kuma baiyana musu cewa, su kalli kansu a matsayin ‘yan jam’iyyar PDP, sannan kuma su bayar da gudunmawarsu wajen samun cigaban jam’iyyar.