Mahukunta a birnin Cologne na kasar Jamus sun amince da mayar wa Najeiya da wasu kayayakin tarihi da aka sace a masarautar Benin tun lokacin mulkin mallaka na Turawan Birtaniya.
Darakta janar na hukumar adana kayayakin tarihi na Najeriya Abba Isa Tijani na daga cikin wadanda suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar mayar wa Najeriya kere-keren tagulla da suka fito daga masarautar gargajiya ta Benin a 1897.
Amma Jamus ta shirya mayar da wadannan kayayyakin Najeriya a shekarar 2023 mai zuwa kamar yadda gwamnatin Jamus din ta sanar.
Ko baya ga kayayyakin tarihin masaurautar Benin, akwai wasu da yawansu ya haura dubu da dari daya da ke jibge a gidajen adana kayayakin tarihi 20 a Jamus.
Sai dai bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar bar wa birnin Cologne wasu kayayakin tarihi 37 a matsayin aro na tsawon shekaru 10.