For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JANYE TALLAFI: Jihohi Zasu Samu Naira Biliyan 5 Kowaccensu A Matsayin Tallafi

Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da naira biliyan 5 ga kowacce jiha da Babban Birnin Tarayya domin su samu damar samar da abincin da zasu rabawa talakawa a jihohinsu.

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ne ya bayyana hakan yau a Fadar Shugaban Ƙasa, Villa, Abuja, jim kaɗan bayan kammala zaman Majalissar Bunƙasa Tattalin Arziƙi ta ƙasa.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci da man fetur a ƙasa, biyo bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

KARANTA WANNAN: Ba Zata Canja Zani Ba, Gwmantin Tinubu Irin Ta Buhari Ce, Ƴan Najeriya Su Shirya Karɓar Ƙaddara

Ƙari a kan wancan, Zulum ya ce, Gwamnatin Tarayyar ta kuma saki motoci biyar-biyar na shinkafa ga gwamnonin jihohi 36 da ake da su.

Da yake ƙara bayani kan yanda abun zai kasance, Zulum ya ce, ana buƙatar gwamnonin jihohin su samar da buhun shinkafa dubu 100, buhun masara dubu 40 da kuma buhunhunan taki.

Ya bayyana cewar, kaso 52 cikin 100 na kuɗaɗen da za a bai wa jihohin kyauta ne yayin da zasu biya kaso 48 cikin 100 wanda zai zo musu a matsayin bashi.

Comments
Loading...