For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JANYE TALLAFI: Ta Ɓaɓe Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC, Yajin Aiki Zai Fara Ranar 14 Ga Agusta

Kusan awanni 24 bayan ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda aka samu yarjejjeniyar dakatar da zanga-zanga, sulhun da aka samu tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya ya wargaje, yayinda aka jiyo ƙungiyoyin na sanar da tsunduma yajin aikin gamagari a ranar 14 ga watan Agusta, matuƙar aka zargi shugabanninsu da saɓa umarnin kotu.

NLC dai ta ɗau matakin ne a dalilin shigar da ƙarar da Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa tai a ranar Laraba, tana neman a tuhumi shugabannin ƙwadagon da saɓa umarnin kotu.

Ƙungiyar ta yi barazanar da zata durƙusar da abubuwa, matuƙar Gwamnatin Tarayya ta gaza janye tuhumar da take wa shugabannin ƙwadagon na ƙin bin umarnin kotu.

Shugaban Ƙungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya sanar da matsayar ƙungiyar a jiya Alhamis ,bayan zaman tattaunawa na Kwamitin Majalissar Zartarwar Ƙungiyar wanda aka yi a Abuja.

A watan Yuni da ya gabata ne, a ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na dakatar da ƙungiyar ƙwadagon ta hanyar Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa ta samu umarnin Kotun Ma’aikata na hana NLC da TUC shiga yajin aiki a kan al’amuran da suka shafi janye tallafin man fetur, tsadar man fetur da kuma matsin rayuwa a ƙasa.

Mai Shigar da Shari’a na Ƙasa kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, Mrs Beatrice Jedy-Agba, a wani jawabi da ta yi, ta yi kira ga NLC da ta dakatar da bayar da wa’adin kwanaki bakwai na shirye-shiryenta na yin zanga-zanga daga ranar 2 ga watan Agusta idan ba a biya musu buƙatunsu ba.

Ma’aikatar Shari’ar ta yi gargaɗi mai zafin ne a ranar 26 ga watan Yuli da ya gabata, inda ta jaddada cewar yajin aikin da ƙungiyoyin suka shirya yi saɓawa umarnin kotu ne, wanda laifi ne da yake jawo ɗauri ga wanda ya aikata shi.

A wajen Gwamnatin Tarayya, irin wannan yajin aikin zai nuna son kai ne, tun da maganar tana gaban kotu.

To amma da take nuna rashin gamsuwarta da yanayin tattaunawar da ake tsakaninta da Gwamnatin Tarayya kan hanyoyin sauƙaƙawa mutane matsatsin da suke ciki da ya samo asali daga janye tallafin man fetur, NLC ta kira zanga-zanga a duk faɗin ƙasa duk kuwa da umarnin kotun da ya hana ta hakan.

Sanannen masanin shari’ar nan kuma lauyan ƙungiyoyin ƙwadagon, Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, ya ce zanga-zangar ba ta saɓawa shari’a ba.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun gudanar da zanga-zangar a ranar Laraba da ta gabata, wadda ta jawo tsaiko ga harkokin kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙi a duk faɗin ƙasa, inda aka rufe bankuna, ofisoshi da kotuna a jihohi da dama.

A ƙoƙarinta na nuna fushinta kan matakin na ƙungiyoyin ƙwadagon, Gwamnatin Tarayya ta garzaya kotu tana neman a tuhumi shugabannin ƙungiyoyin da saɓa umarnin kotu, abin da ya sa ƙungiyoyin ƙwadagon yin barazanar shiga yajin aiki a duk faɗin ƙasa daga ranar 14 ga watan Agustan nan, idan har Gwamnatin Tarayyar ba ta janye ƙudirinta da ke gaban kotun ba.

Comments
Loading...