For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JANYE TALLAFIN MAN FETUR: Noman Shinkafa Ya Tumurmushe A Jigawa

Daga: Ahmed Ilallah

Duk da tunannin akasarin masana, na nuni da cewa cire tallafin mayin fetur shine mafi alkhairi da cigaban tattalin arzikin Nijeriya, kuma zai bawa gwamnatoci makudan kudade domin aiyukan raya kasa.

Amma fa rashin kyakyawan tanaji, ga al’amuran da suke jigo ga tattalin arzikin irin su noma, al’amuran zai kasance tamkar tufka ce da warwara, musamman ma a fagen yaki da talauchi da kuma yaki da yunwa.

Cigaban zai iya kasance wa ne, kawai a wurin shugabannin, amma talakawa na jin kuda.

Ko da yake, yawan mutane suna takaita matsalolin da Yan Nijeriya zasu fuskanta a sanadiyar cire tallafin mayin fetur  kan harkokin sufuri da hauhawar furashi, amma fa, akwai tarin matsalolin da ba kawai talaka zata shafa ba, har da manyan manufofin gwamnatin, musamman a kan noma da yakar yunwa.

Gwamnatin Nijeriya, da fito da manufofin bunkasa noma da yakar yunwa, wanda har ya sanya shugabannin baya garkame boda don hana shigowa da abinci domin Yan Nijeriya su noma da kansu.

Jihar Jigawa na daya daga cikin jahohin da suka fi noman rani a Nijeriya, wanda noman shinkafa yake kan gaba, kusan za a iya cewa a arewacin Nijeriya, Jigawa na kan gaba wajen noman shinkafa. Duk da kasancewar a kwai wurin noman rani na zamani, wato irrigation scheme na gwamnatin tarayya a yankin Hadejia, gudunmawar wannan wuri wajen noman shinkafa a Jigawa kadan ne, bisa la’akari da dubban manoman da suka dogara da injin ban ruwa ne.

Wannan aiki da a ka soma shi tun 1979 sai a bana ne a ke shirin gama kashi na daya na wannan aikin. Da a ce shugabannin baya sun bawa ire-iren wannan auyuka muhimmanci a fadin kasar nan, da bunkasar noman yafi haka.

Kashi 80%, na masu noman rani a jigawa, suna amfani ne da Injinan Bayi masu amfani da Mayin Fetur, wajen bayin ruwa walau ta hanyar kogi ko kuma a rijiyoyi, in banda manoma a karamar Hukumar Auyo, babu wasu manoma da suke amfani da hanyar ban ruwa ta zamani.

A kananan hukumomin da suka fi noman shinkafa a Jihar Jigawa, irin su Kiri Kasamma da Guri duka suna amfani da rijiyoyi, gulbi da koguna ne wajen yin ban ruwa.

Akasarin manoman nan sun dogara da Mayin Fetur ne wajen ban ruwa, dadi da kari ga tashin gwauran zabin da kayan noma irin su takin zamani da maganun feshi sukayi.

A kiyasa, a shekaru biyu baya, manomi kan iya noma Aika Daya ba tare da ya kashe dubu saba’in ba, amma a bana yakai sama da dubu dari da saba’in, wanda a wanna yanayi na cire tallafin mayin fetur, a kalla sai an nunka wannan kudi, domin noma aika guda.

Ayar tambayar ma a nan shine, shin kananan manoman mu na da jarin yin wannan noma? Shin in sun iya yin noman, zasu iya fita har su samu riba?

Shawara ga gwamnatoci, ya zama dole su sanya matsalolin masu noma a cikin kaluballen da cire wannan tallafin zai kawo. Dole hukumomi su yi da gaske, in har da gasken a ke wajen samarwa da wuraren noma na zamani.

A bangaren Jigawa ta gabas, ya zama wajibi da a gaugauta kammala aikin Hadejia Irrigation scheme, kashi na biyu da na uku.

alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...