Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ta bayyana cewa, yin rijistar jarabawar JAMB na shekarar 2022 ba zai samu da wuri ba saboda matsalolin da suka fi karfinta.
Hukumar ta kuma kare kudirinta na amfani da shaidar zama dan kasa, NIN wajen yin rijistar ga duk mai son rubuta jarabawar.
Mai magana da yawun hukumar, Dr. Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan ne a wata hira da yai da jaridar PUNCH a Abuja.
“Mafiya yawan shirye-shiryen da ake kafin lokacin jarabawa, ciki har da rijistar UTME ta 2022, sun makara saboda wasu matsaloli da suka fi karfinmu. Muna shirye wajen yin duk mai yiwuwa ba kawai don mu yi jarabawar ba, har ma da kokarin mayar da rijista da jarabawar UTME ta 2022 mafi inganci,” in ji shi.
Hukumar ta kuma sanar a labaranta na sati-sati na ranar Litinin din nan cewa, hukuncinta na amfani da NIN wani tsari ne na kawo canji domin a magance magudin jarabawa.
Dr. Fabian ya ce “Bullo da amfani da NIN a rijistar UTME ta 2021 wanda hukumar ta yi, wani tsari ne na kawo canji da kuma magance magudin jarabawa. Ya kamata a lura, hukuncin yin amfani da NIN wani hukunci ne mai wahala saboda matsaloli da kalubalanta daga bangarori da dama.
“Sai dai kuma, hukumar ta hango alfanun da shigo da NIN din yake da shi, ta zabi hukuncin da ba a so amma kuma mafi amfani, sanin cewa duk wata sabawa al’ada da za ai sai ya fuskanci kalubale, to amma hakan ba zai sa hukumar ta kasa cimma kudirinta ba.”