Daga: Ahmed Ilallah
Duk da kasancewar ita jigawa da rigimar siyasar ta, ta kan sha banban da wasu jahohin na Arewa, akasarin rigingimun siyasar manyan jama’iyyun Jigawa kan faru ne a gaf koma a lokacin fidda dan takara ko magajin gwamna, a kance tsiyar nasara sai zashi gida, ko kuma yayin da igiyar zaton manya da yaran yan siyasar ta tsinke wa wasu a lokacin da mai mulki ya karkata ga wanda ya ke so.
Za ka iya gaskata wannan batu a shekarar 2014 zuwa da 2015 kafin APC ta kwace ragamar mulkin da ga hannun PDP, mun shaida yadda jigogin yan PDP da yaran su suka gujewa jama’iyar a lokacin da tsohon gwamna Sule Lamido ya tabbatar da cewa Malam Aminu Ringim ne Dan Takara, daga cikin manyan PDPn lokacin har akwai yan Kungiyar Tabare, wanda wannan dalilin ne ya kada PDP a 2015. Amma abin tambaya, shin irin wannan zai iya faruwa a APC? Yayin da aka ce shima Badaru ya kawo dan takarar da ya sabawa ra’ayin jagororin siyasar.
To, yanzu ma lokaci yayi, kuma tuni irin wannan hatsaniya ta siyasa ta soma yamitsa hazo, da dukkan alamu, mutanen da ake ganin baki ya karkata garesu wajen karbar sitiyarin Badaru, akwai rina a kaba wajen karbuwar su a wajen jigogi, jagorori da ma kartikan yan siyasar. A waje guda kuma shi kan sa gwamnan sai yayi lissafin waye nasa ko dansa da zai rike masa amana don gudun kitso da kwarkwata, wanda yin wannan kuskuren shi yafi komai sauki a siyasar Nijeriaya.
Dadi da kari kuma a kwai tunani chanja akalar jagoranci zuwa ga masu jini a jika, maimakon dattijai, to koma menene sai fa anyi dogon lissafi in har za’a iya kaucewa wadannan matsaloli, don gudun maimata yanayin PDP a 2015.
Nazari da bincike na siyasa yana nuna cewa, da yiyuwar a sha mamaki wajen wanda zai iya darewa buzun gwamna Badaru, domin gujewa faduwar tasa irin wanda Lamido yayi a baya, zai yi wahala Badaru yayi lissafi da alkaluman da mutane za su bashi wajen nemo magajin sa, kuma shima kamar sauran gwamnono zai kafa yayan sa ne don samawa kansa makoma a nan gaba, domin an ce da ganin na gaba a ke gane zurfin ruwa. A yau dukkan alamu sun nuna haka, tun daga kan zaben shugabannin jama’iyya da ya gabata daga daga matakin ward zuwa jaha, kai harma da kasa baki daya.
In har gwamna Badaru ya gamsu da baiwa Arewa-Maso-Gabas takara, a wannan yayan nasa na gaba-gaba wa zai iya gadarsa:
Malam Kashifu Inuwa, wanda ba sai anyi dogon turanci a kansa ba, yau a Nijeriya yana daga cikin sannan nun matasa kuma kwararru da kasar nan ke tunkaho da su, wanda ya zamanto sanan ne tun lokacin da ya zama mai taimakawa Minista Isah Ali Pantami lokacin da yake DG na NITDA, wanda daga baya ya gaje shi, ya zamanto dignitaries.
Hukumar NITDA tayi shuhura da kawo sauye –sauye a cikin harkar ilimin fasahar sadarwa a wannan kasa, shigowar sa cikin al’umma da kuma kara karfin sa cikin harkokin siyasar APC ba kawai a yankin da ya fito ba, a ma fadin jihar jigawa, wannan ya nuna rade-radin cewa shima yana cikin wanda ake ganin na iya zawarcin wannan kujerar, musamman ma yadda kusancin sa kullum karuwa yake a wajen gwamna.
Sai dai nazari ya nuna, shin ka iya cewa Kashifu dan gwamna ne? Domin fa shi gwaman a kwararre ya same shi kuma fittace, tafiya iri dayace ta hada su ta Baba Buhari har a ka samu wannna kykkyawar dangantaka, amma koma menene yin ‘da a siyasa ba abu ne mai wahala ba.
Hussaini Mohammed Rally, kamar maigidan sa Badaru shima kwararren Akawu ne, wanda yayi takarar Sanata a Jigawa Northeast a shekara 2019, kuma yanzu shine babban akawun Babbar Kwalejin Ilimi da Shari’a da ke garin Ringim, wanda ake ganin duk cigaba da daukakar da makarantar ta samu fiye da suran takwarorin ta jihar, sun samu ne dalilin fada da jinsa a wurin gwamnati.
Nazari da bincike ya nuna kusan shine na farkon mai kusan ci da Badaru a cikin matasan a siyasance, sun kasan ce tare tun daga DPP, ACN har zuwa APC, duk da ba ya rike da wani mukami, amma ya zamanto mai fada a ji a cikin wannan gwamnati, wand harshahe ya nuna cewa a kwai iyuwar zama daya daga cikin wanda zai iya zawarcin buzun gwamna Badaru.
Barrister Abubakar Sadiq Jallo, wanda Dan Majalissa ne a Majalissar Dokokin Jihar jigawa, mai wakiltar cikin garin Hadejia, wanda kafin zuwa majalissa shine babban sakataren tara kudaden haraji ta jahar jigawa wato Jigawa State Revenue Services, wanda shima dangantakar sa da Gwamna Badaru tayi karfi a wannan lokacin, wanda a yanzu a na ganin babu wani na gaban goshin gwamna kamar Jallo, allamu sun kara tabbata ta yadda aka ga shine a kan gaba wajen yiwa gwamna shidima, mussamman yayin babban taron jamaíyar APC wanda ya gabata a Abuja.
Honourable Jallo ya jagoranci manyan aiyuka na siyasa kamar zaben cike gurbi da akayi a Garki/Babura, K/Hausa da Gwaram, wadan nan alamu dama wasu dalilai, da kuma yadda a yanzu yake chanja salon siyasar sa, na nuna cewar Hon. Jallo kan iya zawarcin wannan kujera.
Musa Shuaibu Guri, wanda a yanzu shine Shugaban karamar hukukmar Guri, wanda kafin haka mataimakin gwamna ne na musamman, kwararren dan siyasa ne kuma makusanci da Gwaman Badaru yana daga cikin matasan yan siyasa masu fada a ji a Jigawa, shigar APC ya chanza salon siyasar Guri.
Musa Shuaibu bisa gamsuwa da Badaru yayi da shi ya kasan ce yana aiyukan Jama’iyar APC jahohi da dama. Nuna karewar sa jagoranci, a matsayin sa na shugaban karamar hukuma, musamman ma Guri wanda ta sha babban da sauran kaananan hukumomi, musamman wajen zaman lafiya, salon shugabancin da ya kawo da kuma kokarin sa na samar da dawwamman zaman lafiya, ya sake fito da shi dandalin siyasar Jigawa wanda ake ganin shima kan iya samun damar zawarcin wannan kujera.
Koma menene, lokacin kadai kan iya warware mana wannan batu, amma alkalimma na nunawa zai yi wahala wanda ba dan Badaru a siyasa ba ya hau buzun sa.
Ahmed Ilallah
Ya Rubuto Daga Hadejia
alhajilallah@gmail.com