Daga: Ahmed Ilallah
Tabbas dukkanin al’ummar da suka dukkufa da adu’a a kan neman cigabansu, kuma suke da kyakkyawar manufa ga jihar su, Allah kan duba al’amuransu, ya yi musu zabi mafi alkhairi da dacewa.
Kamar yadda ita siyasa kan ba da dama ne ta yanci, na zabar jagora, wanda dimokaradiyya ce kadai kan bada ‘yanci da damar fitowa domin a zabeka, amma a karshe kowa ce irin tabukawa da gwagwarmaya a kasha dai, kawai zabin Allah ne zai tabbata.
Malam Umar Namadi, tsohon Kwamishanan Kudin Jihar Jigawa kuma Mataimakin Gwamna a yau, ya zamanto tamkar aya ce a jagororin Jihar Jigawa , haka zalika samun nasararsa ma a wannan karon tamkar wata aya ce Allah ya nuna mana, cewa shine yafi kowa cancantar gadon buzun Gwamna Badaru.
Koda a lissafi irin na mulki a tarihance da kuma a aikace, dukkanin mai bibiyar nasarori da Gwamna Badaru ya samu a jogorancin Jihar Jigawa na shekara bakwai da kwanaki, tabbas Danmodi yana kan gaba wajen dakarun da suka tallafawa gwamna samun wannan nasarar.
Kadan daga ciki, Gwamna Badaru ya yi fice wajen tsantseni da tassarifin kudin al’umma, wanda har ake masa ikirari da Baba Mai-Kalkuleta, to amma fa kashin bayan lissafin kalkuletar da ma ba da shawarar lissafin tana wajen Kwamishinan Kudi, kuma babban mai bawa gwamnati shawarar tassarifin kudinta da kuma yadda ake kashe shi.
Ba karamin dace da sa’a Jihar Jigawa ta yi na samun kwararru, masana kudi guda biyu ke jagorantar jihar ba, wannan ya sanya suka yi fice wajen iya lissafi da kiddigar kashe kudi.
A takaice, banda Maigirma Gwamna, Danmodi ya fi kowa sanin abin da ke shigowa da fita cikin lalitar Jihar Jigawa, a kasancewarsa Kwamishinan Kudi, kuma kwararren akawu, kuma masanin tattalin arziki, babu shakka mutanen Jigawa sun yi tunani mai kyau wajen amince masa yin jagorancin jihar domin bunkasa tattalin arzikin ta.
Gwamna Badaru da Jigawa har yau sune kan gaba a jihohin Nijeriya wajen ingancin kasafin kudi, Jigawa ta samu lambobin yabo masu yawa, harma da tikwici a kan ingancin kasafin kudi wato (Budget), Malam Umar Namadi a matsayin sa na Kwamishina a baya, jagorancinsa ne ya kawo sabon tsare-tsare na zamani wajen shiryawa da aiwatar da kasafin kudin a wannan jiha, wanda har gobe yan Jigawa na alfahari da wannan ci gaba.
Malam Umar Namadi, tabbas ya samu shaidar kafatanin yan siyasar Jihar Jigawa ba kawai yan APC ba har ma da sauran yan jamaíyyun adawa cewa mutum ne kwararre, masannin tsare-tsaren gwamnati, kuma mutum ne mai nutsuwa, hakuri da sanin ya kamata, mutum ne wanda kawai Jigawa ce a gabansa, bai son nuna banbanci ko san kai, wannan ya sanya a kowane lokaci jagororin Jigawa ne ke sanya shi a gaba a dukkan al’amari irin wannan, bai fitowa da sha’awarsa fili.
Malam Umar Namadi, wanda al’umma suka jawoshi cikin harkokin siyasa sabo da kykkyawan halin son taimaka wa al‘umma, musamman matasa a cikin harkar ilimi da dogaro da kai, wannan aiyuka nasa ne ya sanya shi fice har aka sanshi a Jigawa, shine mutum na farko da ya yi kamfanin sarrafa shinkafa, ba kamfanin hukuma ba wato kamfanin Danmodi a fadin Jihar Jigawa. Wannan kamfanin ya samawa dubban mutane aiyukan yi na kai tsaye da kuma na nesa wato (Direct and Indirect Labour) kasancewar kamfanin yana yankin da aka fi noman shinkafa da sarrafa ta, wannan ya bude wa mutane idon dabarun zamani na sarrafa shinkafa.
Tarayyar Danmodi da Gwamna Badaru, a yau dabarun mulkinsu da kishin al’umarsu ya sanya Jihar Jigawa a kan gaba a fadin wanna kasa wajen yawan masana’antun sarrafa shinkafa da ma nomanta.
Malam Umar Namadi, kafin wannan amincewa da ya samu daga dukkanin yan Jama’iyyar APC na yi musu takara a shekara ta 2023, zamu iya tunawa a shekarar 2019 a lokacin da jama’iyyar take neman wanda zai zamanto Mataimakin Gwamna bayan da Senator Ibrahim Hassan Hadejia ya gama wa’adinsa kuma ya tafi takarar Senator, mutane da yawa sun nemi damar darewa wannan kujera, amma bisa adalcin Gwamna Badaru sai ya mikawa masu ruwa da tsaki na Jama’iyyar APCn Jigawa da su sama masa wanda yafi dacewa da yi masa mataimaki.
Domin kasancewar Danmodi wata aya ce a cikin al’umma, masu ruwa da tsakin APC a wannan lokacin sai suka ga Malam Umar Namadi ne ya fi kowa dacewa da zama mukaddashin Gwamna a wannan lokacin, wannan kadai ya ishe mu, mu aminta da dacewar wannan bawan Allah ya zamanto Gwamnan Jigawa a zabe mai zuwa.
Malam Umar Namadi, tamkar aya ce a Jihar Jigawa, a kowane lokaci bai cewa ko nunawa mutane, “ni na dace, ko ku bani, ko ni zan iya, a a” mutane ke nunawa da cewa shine ya cancanta da yazo ya yi ko ya jagoranta.
Allah mun gode maka, Allah ka ci gaba da yi wa Jigawa zabi na alkhairi, domin alkhiarinKa shine alkhairi.
Ahmed Ilallah ya rubuto daga Hadejia