Kungiyar Tuntuba ta Jam’iyyar PDP (PDP Consultative Forum) a Jihar Jigawa ta jaddada goyan bayanta ga Mustapha Sule Lamido a matsayin ɗan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a Zaben 2023 dake tafe.
Sakataren Yaɗa Labarai na kungiyar, Comrade Baffa Danhaya Birnin Kudu ne ya sanarwa manema labarai hakan, bayan gabatar da taron da suka yi a karshen satin da ya gabata a Babban Birnin Jihar, Dutse.
Baffa Danhaya ya ce “Wannan taro an gudanar da shi ne domin karbar rahoto na dukkanin yankuna na sanatoci da muke dasu guda uku a fadin Jihar Jigawa wadanda ya kunshi kananan hukumomi guda 27.
“A cikin rahoton da muka karba ya nuna cewar insha Allahu Jam’iyyar PDP ita ce zata yi nasara a zaben dake tunkaromu. Saboda haka wannan kungiyar ta ke kara Jaddada goyan bayanta ga Alh. Mustapha Sule Lamido domin ya amince yayi takarar Gwamna a 2023, kuma insha Allahu zai amsa kiran al’ummar jihar da suke ta irin wadannan kiraye-kiraye a gareshi”
Baffa Danhaya ya ƙara da cewa, “Kamar yadda kowa ya sani Alh. Mustapha Sule Lamido, yana da farin-jinin matasa da dattawa, ‘yan-boko, ‘yan-kasuwa da dukkanin rukunin al’ummar dake fadin jihar baki daya.
“Mustapha Sule Lamido, mutum ne jajirtacce, dan-kasuwa, dan-boko kuma dan-siyasa.
“Kungiyar Tuntuba ta PDP wadda Alh. Muhd Isa Duniya Bahutu yake shugabanta ta yi gangami ranar 1 ga watan Janairu 2019 a garin Bamaina, taron da wata kungiya ba ta taba yin irisa ba, domin kaiwa Jagoranmu Alh. Sule Lamido ziyarar ban-girma a karkashin tsohon shugabanta Alh. Kabiru Nura Husaini, wanda yanzu shi ne Shugaban Matasan PDP na Jihar Jigawa” a cewar Comrade Baffa Danhaya Birninkudu Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar.