For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JIGAWA 2023: Santuraki Ba Yaro Ba Ne, Ingantaccen Matashi Ne Kamar Dai Gwamna Rimi Lokacin Da Yai Takara

Ina mamakin masu cewa wai Santuraki yaro ne, duk da dai ni a wajena kasancewa yaro ba matsala ba ne, domin kuwa kowa ka ga ya girma a baya da yaron ne, kuma wadanda ake kallon yaran da damansu sun kawowa al’umma ci gaba a fannoni da dama na rayuwa. Sai dai kawai, shi Santurakin ba yaron ba ne a yanzu ballantana a ce masa yaron, shi ingantaccen matashine wanda ya mori lokacin yarintarsa ya kuma sami gatan tasowa cikin kyakkawar tarbiyya da kishin al’umma.

Masu sukan Santuraki da karancin shekaru, idan har su ma sa’anni ko kannen Santurakin ne a shekaru to da alama ba su yarda da kwarin tasowar kansu ba ne, ko kuma suna jin cewa, masu hakkin taso da su ba su yi kokarin da ya dace ba, ko kuma sun kasance matsorata irin wadanda Shata yake ce wa “matsoraci ba ya zama gwani kowa ne ne, kuma ko dan wa” a kan su. Idan kuma sun kasance manya masu shekaru sama da na Santuraki, to da alama ba su iya sauke nauyin da ya hau kansu na tarbiyantar da wadanda ya kamata su tarbiyantar ba, ba su koyar yanda ya kamata su koyar ba, ko kuma son zuciya ya lullube su sun manta cewa lokacin da suna da shekaru irin na Santuraki ya kwarin guiwarsu da karfin iyawarsu suke, ko kuma su ma ba su sami gatan samun tarbiyyar da ta kamata yayin tasowarsu ba, ko kuma dai suna so su cigaba da danne hakkin mafiya rinjayen al’umma wato yara, samari, ‘yan mata, da matasa. Idan kuma ‘yan siyasa ne masu kokarin fifita wani a kan Santuraki to ya kamata a cire musu sunan ‘yan siyasa a kira su da ‘yan jagaliya – domin kuwa masu shekaru irin na Santuraki da kannensa sune mafi rinjayen masu kada kuri’a, amma wadannan ‘yan jagaliya sun zo suna kiransu da wawaye wadanda ba su san me suke ba. Shin ta hanyar zaginmu zaku ci nasara a kanmu? Ta hanyar rena kishinmu ga jiharmu zaku kiramu mu bi ku? Ta hanyar wulakanta tunaninmu, iliminmu, hikimarmu da gundunmawarmu zaku ribace mu? Tabbas duk wanda ya ce Santuraki yaro ne, to ya aikatawa kaso 90 cikin 100 na mutanen Jigawa laifi ta hanyar renasu da ci musu mutunci – ma gani idan tusa zata hura wuta.

Amma kuma akwai wadanda aka yaudaresu, aka sanar dasu labari a bai-bai mai lullube da son zuciya da yaudara da kuma kage, kawai domin yada manufar kin mutanen kirki masu kishin ci gaban al’umma na hakika domin a samu damar ci gaba da shimfida zalunci, ci da ceto, danniya da nuna rashin kishin al’umma. Irin wadannan mutane da suka tsinci kansu a wannan hali na mayaudara, zasu sauya yardarsu idan har suka sami waraka daga duhun da mayaudara suka jefa su a ciki – ma’ana zasu gane cewa Santuraki ba yaro ba ne, Ingantaccen matashi ne wanda zai ciyar da Jihar Jigawa gaba idan har ya ci zabe.

Haka kuma dai, baya ga wannan reni da wulakanci na wadancan marassa kishi, ‘yan ‘wayon a sha’ da neman tabbatar da danniya da yaudara a kan mutanen Jigawa, akwai kuma alamun jahilci da rashin sanin tarihin siyasar Jigawa, Najeriya balle ma ta duniya. Suna gina ilimin siyasarsu ne kan son zuciya da hirar gindin bishiya ba tare da yin nazari na me ya faru a baya ba kuma wacce irin nasara aka samu ko matsala domin a sami damar yin abun da ya dace a inganta yanzu da gobe ba. A tarihin siyasar mutanen da suka sami ci gaba, irin wadannan marassa ilimin tarihin ba sa taba samun dama, domin kuwa babu abin da zasu iya tsinanawa na alheri idan suka wuce gaba.

A taken rubutuna, na kwatanta Santuraki da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kano, aminin mahaifin Santuraki, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi saboda kamancecceniyar da suke da ita ta shekaru a lokacin da suke takara. Duk mai bibiyar tarihi ya san cewa, Gwamna Rimi ne gwamnan Jihar Kano na farko a tsarin demokaradiyya a lokacin Jihar Kano na da girman kasar da ya mamaye jihohin Kano da Jigawar yanzu, wadanda suke kunshe da kananan hukumomi 71 a yanzun. Ba tare da waiwayen aiyukan Rimi ba, na san idan ana bibiyar tarihi, za a san cewa, gwamnonin da akai a Kano bayansa kawo yanzu duk kokari suke su kwatanta ko rabin abun da ya yiwa tsohuwar jihar ne. Ya yi aiki tukuru na gina harkokin ilimi, lafiya, noma, sana’o’i, kasuwanci da kuma tabbatar da hadin kan al’umma.

An haifi Alhaji Muhammad Abubakar Rimi a shekarar 1940 a garin Rimi na Karamar Hukumar Sumaila, ya kuma karbi rantsuwar fara aiki a matsayin Gwamnan Jihar Kano a watan Oktoba na shekarar 1979 lokacin yana da shekaru talatin da tara (39) dai-dai. A wannan lokacin akwai ‘yan siyasa da dama kuma na kusa da mai gidansa Malam Aminu Kano wadanda suka fi shi shekaru da ma shiga gwagwarmayar siyasa, amma Malam Aminu Kano ya amince da cewar Gwamna Rimi ne zai yi wa PRP takara kuma zai iya tabbatar da manufofin alkhairi na jam’iyyar ga talakawan Jihar Kano – abun da ya zama ‘gani a kasa’ bayan Rimin ya yi gwamnan a Kanon, gwamnan da ya zama abun alfaharin dukkanin mutanen tsohuwar Jihar Kano, kuma muke cin moriyar hakan har kawo yanzu.

Malamin Gwamna Rimi da mahaifin Santuraki, Sule Lamido wato Malam Aminu Kano, kwararren dan siyasa ne kuma shaharre a Najeriya, Afirka da ma duniya. Duk wani dan Najeriya musamman ma yankin Arewa, Malam Aminu Kano ya yi masa gata, domin kuwa yana kan gaba-gaba cikin masu gwagwarmayar kwato yancin talaka da ma dukkanin bakar fatar Afirka daga hannun Turawan Mulkin Mallaka da sauran masu danniya wa al’umma. Dan NEPU ne da tarihi ya nuna cewar, ba don ita NEPUn ba da talakan Arewacin Najeriya ya zama bawa na har abada.

Malam Aminu Kano ya yi shuhura da suna a gwagwarmayarsa a dukkan fadin Najeriya tun shekarunsa suna kasa da talatin. A shekarar 1959 aka zabi Malam Aminu Kano a matsayin dan Majalissar Najeriya lokacin yana da shekaru talatin da tara (39) dai-dai a duniya, domin kuwa an haife shi ne a shekarar 1920 a unguwar Sudawa da ke birnin Kano. Kuma wannan majalissa ta su Malam Aminu Kano ita ce ta wuce gaba wajen tabbatar da samun ‘yancin Najeriya a shekarar 1960, sannan kuma yana kan gaba-gaba wajen wannan gwagwarmayar karbo ‘yancin da aka samu nasara lokacin yana da shekaru arba’in (40) a duniya.

Akwai misalai da dama na tarihin ‘yan gwagwarmayar da sukai shuhura wajen ceton al’umma a da da yanzu, a Najeriya da kasashen duniya wadanda duk shekarunsu ba su kai 40 ba lokacin da suka bayar da wannan gudunmawa. Saboda haka, rashin sanin tarihi ne da son zuciya, da kuma rashin kishin al’umma da ma yunkurin tabbatar da danniya da fatan samun koma bayan al’umma – mutum ya ce wa dan shekara 39 yaro idan an nemo shi ya jagoranci al’umma. Mustapha Sule Lamido (Santuraki) ba yaro ba ne, domin kuwa a yanzu haka shekarunsa 39 kamar dai na Rimi lokacin da yai takara da na Malam Aminu Kano lokacin da ya je Majalissar Najeriya. Haka kuma Santuraki magidanci ne, mai mata biyu da ‘ya’ya, sannan kuma mai ilimi ne domin a wadannan shekaru ya samu nasarar yin digiri har hawa uku. Kari a kan haka, Santuraki dan gata ne, domin kuwa yana da kwararren dan siyasa, sananne a duk fadin Najeriya wajen kishin talaka da kwato masa ‘yanci, Sule Lamido a matsayin baba, jagora kuma abun koyi, kamar dai yanda Rimi ya samu gata daga Malam Aminu Kano lokacin da yai Gwamna.

Abun farinciki shine, ‘yan kalilan ne masu wancan karamin tunani na duban shekaru wajen yanke hukunci, amma mafi yawan al’ummar Jigawa sun gamsu da nagarta da kuma cancantar Santuraki a matsayin wanda zai jagoranci jihar a shekarar 2023, saboda Allah ya hore masa dukkan abubuwan da ake bukata ga gwamna na nagarta, kama daga imani, ilimi, hankali, kishin al’umma, jajircewa da kuma mashawarta na gari.

Malam Kabiru Sufi

Ya rubuto daga Birnin Kudu, Jihar Jigawa

Comments
Loading...