Daga: Ahmed Ilallah
Tabbas, lokaci ya yi da mutanen Jigawa kimanin miliyan biyar suke da muradin wanda zai zo ya dora tafarkin gina jihar da gwamnonin baya suka dauko.
Duk mutumin da ya san Jigawa a shekarar 1991 da aka kirkire ta da kuma Jigawa yau, zai yiwa Allah godiya, zaikuma godewa gwamnoninmu na baya, bisa kishinsu da aiki tukuru.
Amma fa, ya zama dole mu zabi dattijo, kwararre, mai hakuri da juriya don ginawa da saisaitawa a inda aka tsaya, ya zama dole mutanen Jigawa suna tunani da irin jihohin da suka dore a kan ginawar cigaba irin su Jihar Legas, wanda kididdiga ta nuna suna kan gaba, bama a Nijeriya ba, har ma a Afrika.
In muka yi tambihi, kadan daga cikin tsari mai kyau da jajircewar shugabannin mu na baya da ya maida Jigawar yau, in muka tuna a yayin da aka yi Jigawa a shekarar 1991, Babban birnin jiharmu Dutse, hatta ma’aikata sai dai su yi jeka ka dawo da ga garuruwansu ko daga tsohuwar jiharmu ta Kano, hatta matsugunnin gwamna ya zame mana kalubale – Amma a yau Birnin Dutse yana daga cikin biranen da ake kallo ta fuskar saurin ci gaba a wannan kasa.
A Jigawar yau, hatta tsoffin jihohi irinsu Bauchi, Yobe, Gombe suna dogara da katafaren filin jirgin saman Dutse wajen jigilolinsu na yau da gobe.
A baya a shekarar 1991 da aka samu Jigawa, babu wata CIKAKKIYAR MAKARANTA guda daya ta gaba da Sakandire, hatta makarantar koyon aikin Jinya babu koda kwalli daya.
Amma a Jigawar Yau, Jami’a (University) ma muna da guda hudu, yau a Jigawa ana karatun Digirin Digirgir banda sauran Kwalejoji da suke karatun digiri duk a Jigawa, ga wasu karin Jami’un guda biyu da suka sami sahalewar gwamnatin tarayya na gudanarwa.
Jigawar yau, muna da manyan makarantun gaba da sakandare mallakar jiha har guda hudu, ga na Gwamnatin Tarayya guda uku. A yau Shugabannin Jigawa na jiya da na yau sun gina mana makarantun koyan aikin jinya guda biyar a Jigawa, makarantun aikin jinya masu zaman kansu, sun kai kimanin guda takwas.
In muka sake tuna baya, a da mutumin Kazaure in yana son zuwa babban birnin jiha wato Dutse sai ya je Kano ya ya da zango kafin ya iya zuwa Dutse, kai wani lokacin ma sai ya ya da zango a Kwanar Hugumar Kano kafin zuwa Dutse.
A da mutumin Maigatari ko Babura in zai je Birniwa sai ya yada zango a Gumel da Hadejia kafin ya isa Birniwa ko yaje garin Nguru Jihar Yobe.
A da mutumin Baturiya, Kadira, Musari ko Abunabo sai ya kwana bai zo Hadejia ba, a tafiyar da bata wuce kilomita talatin ba, amma a yau mutanen wannan yankin sun maida Hadejia tamkar unguwa, kusan babu wani yanki a wannan jiha da ba shi da makamanciyar wannan matsala. Amma a yau a kwai hanyoyin mota santal da suka kewaye Jigawa. Kiddiga ta nuna wannan gwmanatin ma ta Gwamna Badaru ta gina hanyoyi sama da kilomita dubu.
A Jigawar yau zamantakewar al ‘ummar jihar ya inganta, tunanin duk dan Jigawa a yau shine wa zai gina jihar, wa zai kawo mana cigaba, wa zai dora mana tsarin cigaban da jihar nan ta dauko?
Jajircewa da hakurin shugabancin gwamnoninmu na jiya da na yau ne ya kawo wannan gagarumin canji a fannin ilimi da lafiya a wannan jiha.
Tabbas ya zame mana dole muyi la’akari da kykkyawan tunani ga wanda zai dora a kan wannan cigaba, zai zamanto burin yan Jigawa yayin da suka amince da DANMODI ya yi musu gwamna, ya dora da kawo canji fiye da yadda na baya suka yi.
Kyakyawan tunanin shugabanin Jigawa na yau na zakulo dattijo kuma jajirtacce a kan ya dora cigaban Jigawa ba karamin tunani bane.
Tarihi ya nuna ba a taba yin zaben cikin gida ba mai cike da yanci da dimokaddiyya kamar yadda akai a fiddo da DANMODI, dukkanin wayanda suka yi takara sun cancanta kuma kwararru ne wanda dukkanin su za su iya kaimu gaci, fito da DANMODI da jagororin APC suka yi tabbas sun nuna wa duniya kishin jiharsu da burin yadda Jigawa za ta zama a gobe, domin so suke a dora a kan Jigawar yau.
A yau zaton mutanen Jigawa a wurin DANMODI bai wuce kyakkyawan tsarin da zai zo da shi da dorawa da manufofi masu kyau don ciyar da Jigawa gaba ba, bunkasa mana babban birnin Jiha Dutse, kawo aiyukan ci gaba a fadin jihar da bunkasa tattalin arzikinta, dadi da kari kawo manufofi masu kyau na sake hada kan mutanen Jigawa.
Jigawa Abar Alfaharinmu!
Ahmed Ilallah, ya rubuto daga Hadejia, Jihar Jigawa