Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana jihar Jigawa a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha a Najeriya yawan wadanda ba su da asusun banki.
Philip Yila Yusuf, Daraktan Sashin Cigaban Kudade na CBN, shine ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a kaddamar da taron amfani da fasahar zamani a harkokin kudade ga mata da matasa, wanda aka gudanar a Dutse, ranar Litinin.
Audu Amadu, Kwaturolan Babban Bankin Najeriya reshen Dutse ne ya wakilci Philip a taron, inda ya bayyana cewa wannan tsari ne na CBN da sauran masu ruwa da tsaki domin habbaka damar wadanda ba su da asusun banki wajen samun biyan bukatunsu na kudade.
Audu ya ce akwai kananan hukumomi biyar cikin ashirin da bakwai da jihar ke da su wadanda babu bankuna a cikinsu.
Ya kuma bayyana cewa wannan taro an shirya shi domin bayar da dama ga wadanda ba su da asusun bankin mallakar asusun kyauta cikin tsawon sati da za a debe ana taron.
Ya bayyana dalilin zabin jihar Jigawa cikin jihohin da za a yi taron a matsayin karfin tsamarin matsalar rashin masu asusun bankunan, inda ya ce yawan masu asusun na tsakanin kashi 10 zuwa 15 ne cikin 100.
Audu Amadu ya kuma ce, “shi yasa muka zabi jihar Jigawa cikin jihohin da za su amfani wannan taro, la’akari da kananan hukumomin da ba su da da bankuna, kamar Kiyawa, Miga, Roni, da kuma Buji da ma sauran”.
Alhaji Umar Namadi, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, shine ya wakilci gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar a taron, ya kuma yabawa Babban Bankin Najeriya bisa tunanin yin taron, inda ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin jihar.
Daga: Kabiru Zubairu