Matasa masu kishin cigaban jihar Jigawa sun kirkiri wata tafiya domin tabbatar da samuwar cigaban jihar a fannonin ilimi, lafiya, tattalin arziki da sauran ababen more rayuwa.
Bayan nazari da duba irin kwarewa da iyawar da masu ikirarin neman zama gwamna a Jihar Jigawa suke da, matasan sun yi ittifakin cewa Tsohon Shugaban Marassa Rinjaye a Majalissar Wakilai, Hon. Farouk Adamu Aliyu shine ya fi cancanta da al’ummar Jihar Jigawa su mikawa amanar jagorantar jihar a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Matasan sun kira tafiyar tasu da FAROUQ23 NEW DOWN PROJECT (FANDOP) wadda ke nufin tabbatar samuwar sabon samfurin cigaban Jihar Jigawa irin wanda ya dace da zamani.
A sanarwar da matasan suka aikowa TASKAR YANCI, sun baiyana cewa, “Mu dandazon matasa ne masu son cigaban Jigawa karkashin Kungiyar Magoya Bayan Farouk Adamu Aliyu, masu manufa irin daya ta samar da nagartaccen shugabanci ga jiharmu a shekarar 2023.
Matasan sun kara da cewar, tafiyar tasu zata bude dama ga matasan Jihar Jigawa wadanda suka kware wajen bayar da gudummawa a tabbatar cigaban tattalin arziki da zamantakewa.
Matasan sun nuna cewa cigaban al’umma na danfare da samar musu da madogara da kuma aiyukan yi, abin da suka amince cewa Hon. Farouk Adamu Aliyu shine mafi cancanta domin tabbatar hakan a Jihar Jigawa.
Sanarwar kaddamar da tafiyar FAROUQ23 NEW DOWN PROJECT ta nuna cewar idan Hon. Farouk Adamu Aliyu ya samu nasarar zama gwamnan Jigawa jihar za ta samu cigaban fannonin harkar lafiya, cigaban tattalin arziki, da kare muhalli, samun shigowar masu sanya hannun jari.
Haka kuma matasan sun nuna cewar jihar za ta samu bunkasar harkar cigaban sadarwar zamani, fasaha da kere-kere da kuma gagarumin cigaba a fannin noma.
Wani abu da matasan suka nuna a matsayin wata nagarta ta Hon. Farouk Adamu Aliyu ita ce yardarsa da biyayyarsa ga tsarin demokradiyya wadda ke baiwa kowa dama iri daya wajen bayar da gudummawa domin bunkasa jihar da ma kasa baki daya.
Kwamared Haruna Isa shine jagoran matasan, ya kuma yi kira ga sauran matasan Jigawa da su zo su hada kai domin tabbatar da cigaban Jihar Jigawa.