Daga: Bala Ibrahim
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce tana asarar sama da Naira Miliyan 100 a duk shekara sakamakon lalata injinan samar da ruwa a fadin jihar.
Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Ibrahim Garba Hannun Giwa ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da kafafen yada labarai wanda kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya ta reshen jihar Jigawa ta shirya a cibiyar Manpower Development institute da ke Dutse.
Ya ce tun farkon gwamnatin yanzu a karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar gwamnatin ta kashe sama da Naira Biliyan 22 wajen samar da tsaftataccen ruwa a fadin jihar.
“A cikin lokacin, mun canza sama da injinan ruwa 284 masu amfani da wutar lantarki zuwa amfani da hasken rana, yayin da aka gina sabbin injinan samar da ruwa masu amfani da hasken rana guda 437”
“An kuma gina rijiyoyin burtsatse guda 4,472 a duk fadin jihar yayin da aka inganta tsarin samar da ruwan birane”
“Muna alfahari da samun kashi 92 cikin 100 na samar da ruwan sha ga al’ummar mu kamar yadda UNICEF ta tabbatar”.
Kwamishinan ya nuna damuwarsa kan sata da lalata injinan samar da ruwan da ke haifar da wahala ga ‘yan jihar da kuma lalata ƙoƙarin Gwamnati na samar da ruwan ga kowa.
“A shekarar da ta gabata kadai an sace fiye da famfuna, batira, da panels har guda 163″
Kwamishinan ya kuma shawarci jama’a da su kasance masu mallakar dukkan kayan aikin Gwamnati a cikin al’ummomin su tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro.