Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya amince da fara aiwatar da sabon tsarin biyan fanshon da aka sabunta gwargwadon amincewa na naira 12,000 mafi karanci a wata.
Shugaban Ma’aikata na jihar, Alhaji Hussaini Ali Kila ne ya bayyana hakan jiya a babban birnin jihar, Dutse.
Ya bayyana cewa, samun amincewar gwamnan ta bayar da damar kara yawan fanshon ‘yan fanshon jihar gwargwadon sabon tsarin.
Ya kara da cewa, sabon karin fanshon zai fara aiki ne a watan Janairu na shekarar 2023 mai kamawa.
Hussaini Ali Kila ya kara bayyana cewa, duk da cewa karin mafi karancin fanshon zai kara nauyin kashe kudade a jihar, gwamnatin jihar ta yarda da cewa, ya kamata ‘yan fansho su sami yanayin rayuwa mai kyau.