For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jigawa Ta Kaddamar Da Shirin Dashen Bishiyoyi Na Bana

Daga: Abubakar Muhammad

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gano ba zata iya samar da ingantaccen aikin gona da sarrafa kayan amfanin gona da kuma kirkiro da masana’antu wadda sune manyan hanyoyin samar da aikin yi musamman ga matasa ba tare da samar da kyakkyawan muhallin da zai tallafa wajen ganin hakan ya inganta ba.

Gwamna Badaru ya ce tun da farko gwamnatinsa sai da ta magance matsalar muhalli da kuma kwararowar hamada, zezayar kasa, ambaliyar ruwa da kuma kawar da ciyawar kachala a fadin jihar.

Haka kuma Gwamnan ya kara da cewa a tsawon shekaru shida da yake jagorantar jihar  gwamanatinsa ta gina magudanan ruwa na sama da kilomita 36 da kuma gina titunan cikin gari a fadin kananan hukumomi 27 dake jihar.

An dai raba irin dashen bishiyoyin ne ga masarautu, kungiyoyin manoma, kungiyoyin masu zaman kansu da kuma daidaikun jama’a a bikin da aka gudanar a garin Maigatari.

A jawabin maraba, kwamishinan Ma’aikatar Muhalli, Ibrahim Baba Chai-Chai a madadin ma’aikatan ma’aiktar, ya bayyana godiyarsa bisa basu damar samar da irin bishyoyi sama da miliyan 12 a tsawon shekaru shida na wannan gwamnatin.

Bishiyoyin da suka bayar da gudunmawa wajen kawar da kwararowar hamada a yankunan kananan hukumomin Kaugama, Birniwa, Gumel da Maigatagari.

Wadanda suka sami damar halartar taron sun hada da sarakuna, kwamashinoni, masu bawa gwamna shawara, yan majalissar jihar. shugabannin kananan hukumomin Gumel, Sule Tankarkar, Gagarawa da ‘yan siyasa da kuma masu fatan alheri.

Comments
Loading...