Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya amince da kirkirar sabbin makarantun Gwamnatin Tarayya guda 2 a jihar Jigawa.
Sanarwar amincewar ta fito ne daga Mai Taimakawa Shugaban na Musamman a kan Harkokin yada Labarai, Malam Garba Shehu a ranar Juma’ar nan.
Makarantun da Shugaba Buharin ya amince da su sune; Federal College of Agriculture, Kirikasamma da kuma Federal College of Education (Special), Birnin Kudu.
Garba Shehu ya kuma ce, Shugaban ya kuma sanya hannun amincewa da Dokar Gyaran Majalissar Binciken Harkokin Noma ta Najeriya (Agricultural Research Council of Nigeria (Amendment) Bill, 2021).