For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jigawa Ta Warewa Asibitin Kwararru Na Birnin Kudu, Kazaure Da Hadejia Biliyan 2

Daga: Kabiru Zubairu

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware Naira Biliyan 12.7 a kudirin kasafin kudin shekarar 2022 domin aiyuka a fannin lafiyar jihar.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar ga ‘yan majalissar jihar na kudirin kasafin kudin shekarar 2022.

Gwamnan ya bayyana cewa mafi yawan adadin kudaden da aka ware za ai amfani da su ne wajen kammala aiyukan da aka fara da kuma sanya kayan aiki a manyan asibitocin da ake ginawa guda biyu da suka hada da Asibitin Kwararru na Hadejia da na Kazaure.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin an yi wadan nan aiyuka da ma aiyuka a sauran manyan asibitocin jihar da kayan aikin asibiti na zamani.

A bangaren lafiyar, gwamnan ya ce an ware Naira Biliyan 6.4 domin karasa aiyukan manyan asibitoci (General Hospitals), yayin da aka ware Naira Biliyan 2.0 ga asibitin kwararru na Birnin Kudu, Hadejia da kuma Kazaure.

Gwamnan kuma ya ce za a kashe Naira Biliyan 1.7 ga aiyukan da suka shafi Lafiya a Matakin Farko (Primary Health Care), kamar ciyar da cibiyoyin lafiya a matakin farko gaba, shiri kan ingantaccen abinci, da kuma tallafi kan aiyukan ceton rayuka miliyan daya na Save-One-Million-Lives.

Haka kuma an ware Naira Miliyan 850 domin samar da kayan aikin lafiya a mazabu, tallafin shirin inshorar lafiya, da kuma shirin lafiya kyauta na mata masu ciki da kananan yara.

An kuma ware Naira Miliyan 800 ga manyan asibitoci domin shirin bayar da magani kyauta ga mata masu ciki da kuma kananan yara.

Gwamnan ya kuma ce za a kashe Naira Miliyan 670 wajen bunkasa makarantun lafiya na jihar da suka hada da College of Nursing and Midwifery Birnin Kudu, School of Nursing Hadejia, School of Health Technology Jahun da kuma School of Midwifery Babura.

Za a kuma kashe Naira Miliyan 280  domin bunkasa sassan kula da masu ciwon ido, masu zazzabin cizon sauro, da kuma kula da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS, da ma shirin kula da cututtukan tarin fuka da kuturta da kuma bunkasa tsarin ajjiye bayanan lafiya.

Comments
Loading...