Gwamnatin Jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin Najeriya ta rufe makarantar Arise and Shine Nursery and Primary School, Asaba bayan zargin malamin makarantar da zane dalibi dan wata 19 da haihuwa, dukan da yai sanadiyyar mutuwar dalibin.
Malamin mai suna Emeka Nwogbo, wanda dan gidan matar da take da makarantar ne, an rawaito cewa, ya zazzane dan karamin yaron ne mai suna Obinna Udeze a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2022 a binda ya jawo jiwa yaron raunuka a jiki.
An baiyana cewa, dan karamin yaron ya rasu a asibitin Federal Medical Center, Asaba a jiya Asabar sanadiyar bulalar da malamin yai masa.
Kwamishinan Ilimin Firamare na Jihar Delta, Chika Ossai, ya fadawa wakilin PUNCH cewa, gwamnati ta rufe makarantar a yau Lahadi.
Ya ce, “Eh, a safiyar yau (Lahadi), gwamnati ta dau mataki, ta kuma rufe makarantar a yanzu. Sannan na biyu da ma ba makarantar da aka amince da ita ba ce.
“Mai makarantar da danta (malamin da yai dukan) suna hanun ‘yansanda, gwamnatin jiha da gaske take a kan lamarin kuma za ta bi shi har zuwa karshe domin tabbatar da cewa duk wadanda suke gudanar da makarantar da ba a yiwa rijista ba sun fuskanci hukunci yanda ya kamata.
“Saboda yana da sauki ka kula da makarantu masu rijista, amma wadanda suka sabawa ka’ida za mu rufe su.
Ya nuna rashin jin dadinsa game da lamarin, a yayinda yai kira ga makarantu da su kula da yanda ake kula da dalibansu.
(PUNCH)