Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba motocin ɗaukar majinyata na zamani ga asibitocin jihar don sauƙaƙa jigilar marasa lafiya zuwa manyan cibiyoyin lafiya.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Alhaji Yunusa Musa Ismail, ne ya miƙa makullin motocin ga manyan likitoci na Manyan Asibitocin Jihar da Asibitin Koyarwa na Kalgo, da ke Birnin Kebbi a yau Talata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa asibitocin da suka amfana daga wannan tallafi sun hada da Asibitin Tunawa da Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, Babban Asibitin Argungu, Babban Asibitin Bunza, Babban Asibitin Yauri da kuma Babban Asibitin Zuru.
Yayin da yake mika makullin, Musa-Ismail ya umurci likitocin da su kula da motocin yanda ya kamata kamar yanda Gwamna Nasir Idris ya umarta.
Ya ce, “Gwamna Idris ya himmatu wajen inganta sashen lafiya, wanda ya hada da saukaka zirga-zirgar marasa lafiya don samun kulawar lafiya, saboda haka aka sayo da kuma rarraba motocin ɗaukar marassa lafiyar.
“Gwamnan ya kuma amince da gyara albashin likitoci don ya dace da yanda ake biya a matakin tarayya domin magance kwararewar kwararru daga aiki.
“Likitoci a jihar sun fara jin dadin sabon tsarin albashi tun daga watan Agusta.”
NAN