For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Jihar Lagos Ta Hana Amfani Da Amsakuwwa A Guraren Taruwar Jama’a

A jiya Talata, Gwamnatin Jihar Lagos ta haramta yin amfani da amsakuwwa ko wani sauti mai kara a tashoshin mota domin a rage yawan hayaniyar saututtuka da ke damun al’umma.

Da yake jawabi ga manema labarai, Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Muhalli na jihar, Dr. Omobolaji Gaji ya ce, yawaitar hayaniyar kararraki musamman a guraren taruwar jama’a na zama abun damuwa.

Gaji ya ce, korafin yawaitar saututtuka shine mafi yawan korafe-korafen da ma’aikatar sa ke karba, wanda ya kai kusan kaso 75% na yawan korafe-korafen da suke karba.

Ya baiyana cewa, hayaniya wadda ke nufin saututtukan da suka wuce ka’ida ta yi matukar yawa a Lagos.

“Matsalar tana jawo damuwa da matsalolin da suka shafi lafiya, sannan wadanda suka dade cikin wannan yanayi, suna fuskantar matsalar ji wadda ba karamar matsala ba ce ga lafiya.”

Babbar Manajar na Hukumar LASEPA, Dr Dolapo Fasawe ta ce, daga ranar Laraba (yau), haramun a kan kowacce tasha ta yi amfani da amsakuwwa wajen kiran fasinja.

Fasawe ta kara da cewa, duk wata tasha da aka samu da karya wannan doka, za ta fuskanci fushin hukuma.

Ta kara da cewa, sashi na 177 karamin sashi na 2 na Dokar Kare Muhalli ta Jihar Lagos, 2017 ya haramta amfani da amsakuwwa wajen kiran fasinja ko tallen hajoji a tashoshi da kasuwanni da sauran guraren taruwar al’umma.

(PUNCH)

Comments
Loading...