Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta samu kudi naira tiriliyan 16.8 a matsayin kudin shiga na jiha a shekarar 2021.
Wannan ya zo bayan jihar ta hana anfani da rasitai na hannu tare da kirkiro da hanyoyin karbar haraji na zamani a jihar.
Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar, Ahmed Muhammed ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da wakilin PUNCH a Lafia a yau Talata.
Ya bayyana cewa, ya zama dole a kirkiro da hanyoyin karbar harajin, saboda amfani da rasitan hannu wajen karbar haraji ya zamanto hanyar da wadansu ‘yan rashawa ke arzuta kansu da kudin jihar.
KU KARANTA: Rufe Twitter Ya Jawowa Najeriya Asarar Sama Da Naira Triliyan 10
Muhammad ya ce, kafin a nada shi a mukamin da yake kai yanzu shekaru hudu da suka gabata, mafi yawan harajin da jihar ta samu shine naira biliyan 6, amma yanzu da kokarinsa na kirkiro da sabbin hanyoyin karbar harajin, jihar ta samu nasarar tattara kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 16.8 a shekarar 2021.
Muhammad ya ce, “adadin harajin da muka samu a shekarar da ta gabata shine naira biliyan 16.8. Mun samu nasarar hakan ne saboda gwamnatin jiha ta hana amfani da rasitan hannu. Yanzu haka muna manhaja da muke amfani da ita wajen tattara harajin.
“Idan ka biya haraji a manhajar, za ka samu damar cire rasitinka ta yanar gizo. Amfani da rasitan hannu, hanya ce da wasu ‘yan rashawa ke amfani da ita wajen sace kudaden gwamnati. Kowa kawai yana buga rasiti a da, amma yanzu da bayyanar sabon tsari, ba za ka samu rasiti ba har sai ka biya ta manhajar da aka tanada.”
Muhammad ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar na hada guiwa da rundunar ‘yansanda da kuma rundunar tsaro ta farin kaya wajen kamo bata gari wadanda har yanzu suke amfani da rasitan hannu suna karbar kudade daga ‘yan jihar duk da an hana hakan.