An kammala gudanar da Gasar Karatun Al’Qur’ani ta Bana Karo na 37, wadda aka gabatar a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Nura Abdullahi Bello daga Jihar Sokoto shine wanda ya samu nasarar zama Gwarzon Shekara na bana, bayan ya samu maki 97.98 cikin 100 a aji na farko wato izu sittin da tafsiri bangaren maza.
Aisha Abdulladif Muhammed daga Jihar Yobe ita ce wadda ta samu nasarar zama Gwarzuwar Shekara ta bana, bayan ta samu maki 96 cikin 100 a aji na farko wato izu sittin da tafsiri bangaren mata.

Jihohin Zamfara da Bauchi sune suka samu nasarar lashe mataki na biyu na gasar, wato izu 60 hadda, inda Muttaka Ishaq Yakubu daga Zamfara ya zo na daya da maki 96.2, yayin da Hassana Muhammad daga Bauchi ta zo na daya a bangaren mata da maki 94.10.
A mataki na uku kuma, Jihohin Kaduna da Nasarawa ne suka yi nasarar samun mataki na dai-dai, inda Umar Bello Kofa daga Kaduna ya samu maki 96.5, sai kuma Aisha Usman Dariya daga Nasarawa ta samu maki 96.30.
Ministan Sadarwa, Dr. Isah Ali Pantami ne ya wakilci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a taron rufe Musabakar, inda ya ce Shugaban Kasar na kira ga al’umma da a rungumi zaman lafiya domin samun ingantaccen ci gaba a kasa baki daya.
Gwarazan sun sami kyaututtukan sabbin motoci daga wajen Shugaban Kasa da Gwamnatin Zamfara da kuma dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu.