Daga: Kabiru Zubairu
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana cewa jihar ta samu Naira Biliyan Dari da Takwas da Miliyan Ashirin da Hudu da Dubu Dari Tara da Arba’in da Uku da Dari Biyu da Arba’in da Shida (N108,024,943,246) tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis lokacin da yake gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 ga majalissar dokokin jihar Yobe.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan adadi shine daidai da kaso 77.23 cikin 100 na adadin kudaden da akai nufin kashewa a kasafin kudin shekarar nan ta 2021.
Mai Mala Buni ya bayyana cewa a aiyukan yau da kullum, gwamnatin ta kashe Naira Biliyan Hamsin da Hudu da Miliyan Dari Hudu da Arba’in da Shida da Dubu Dari Tara da Casa’in da Bakwai da Dari Tara da Saba’in da Takwas (N54,446,997,978) cikin Naira Biliyan Saba’in da Daya da Miliyan Dari Takwas da Hamsin da Hudu da Dubu Dari Biyu da Sha-daya da Dari Bakwai da Sittin da Bakwai (N71,854,211,767) da ake sa ran kashewa a bangaren cikin shekarar da muke ciki.
Wannan adadi ya nuna samun nasarar aiwatar da aiyuka a bangaren aiyukan yau da kullum da kaso 75 cikin 100.
A bangaren manyan aiyuka kuma, gwamnan ya bayyana cewa an kashe Naira Biliyan Talatin da Takwas da Miliyan Dari da Sittin da Takwas da Dubu Dari Takwas da Sha-Daya da Dari Uku da Sittin da Hudu (N38,168,811,364) cikin Naira Biliyan Sittin da Takwas da Miliyan Ashirin da Dubu Dari Biyu da Tamanin da Takwas da Naira Tara (N68,020,288,009) da aka warewa bangaren.
Wannan adadi ya nuna samun nasarar aiwatar da aiyuka a bangaren manyan aiyuka da kaso 56.11 cikin 100.
Gwamnan ya bayyana cewa duk da matsalolin matsin tattalin arziki da ake ciki, jihar ta samu nasarar aiwatar da aiyuka a kasafin kudin shekarar 2021 da kaso 66.21 cikin 100.