Gwamnatin Jihar Zamfara ta canza matsugunnin sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima na wucin gadi daga Tsafe zuwa Gusau saboda taɓarɓarewar tsaro.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Hassan Muhammad Gusau ne ya sanar da hakan lokacin da yake tarɓar Darakta Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar M K Fadah.
Mataimakin Gwamnan ya yi takaitaccen bayani kan yanayin matsalar tsaron da jihar ke ciki, inda ya sanar da Darakta Janar din cewa ana samun ci gaba a yakin da ake da ɓatagari a hankali, inda ake ci gaba da samun zaman lafiya har mutane na komawa yanayinsu na da.
Mataimakin Gwamnan ya ƙara da baiyana cewa, gwamnatin jihar ta bi tunanin NYSC na dakatar da horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihar saboda matsalolin tsaron da suka rinƙa faruwa a jihar a lokutan baya.
Ya kuma baiyana yanayin da aka tsinci kai a cikin a matsayin abin takaici, inda ya ce, Gwamna Bello Matawalle ya bayar da umarnin samar da abubuwan da ake buƙata domin canzin matsugunnin ta yanda za a ci gaba da harkokin NYSC a jihar kamar sauran jihohin Najeriya.
Da yake taya sabon Darakta Janar na NYSC murnar naɗinsa da akai, Mataimakin Gwamnan ya tabbatar wa daraktan shirin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an samu nasarar gudanar da sauyin sansanin cikin nasara.
Lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar M K Fadah ya ce, sun zo jihar ne domin su duba gurin da aka ware domin mayar da sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidimar a jihar Zamfara.
Darakta Janar ɗin ya ƙara da cewa, matsalar tsaro matsala ce da ta shafi duniya gaba ɗaya ba iya Najeriya ba.