Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a boye a wata ziyara da Jonathan din ya kai Fadar Shugaban Kasar bayan kammala zaman majalissar zartarwa ta kasa wadda Shugaba Buhari ya jagoranta.
Rahotanni sun ce Tsohon Shugaban ya isa Fadar Shugaban Kasar ne da misalin karfe 4:00 na yamma, ya kuma gana da Shugaban a boye ba tare da barin ‘yan jaridu sun san me aka tattauna ba.
Bayan kammala ganawar, Tsohon Shugaban Kasar, Goodluck Jonathan bai gana da ‘yan jaridu ba, haka su ma bangaren fadar Shugaban Najeriyar ba su magantu kan ganawar ba a lokacin da muka wannan rahoton.