Jihar Kaduna ta sanar da cewa za ta kori malaman makaranta 233 wadanda suka gabatar da takardun bogi daga aiki.
Shugaban Hukumar Ilimi Matakin Farko na jihar, Alhaji Tijjani Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a Alhamis.
Shugaban ya ce yana daya daga cikin aiyukan hukumar, tabbatar da cewa duk malaman makaranta suna da takardun da suka ce suna da su.
Hukumar ta kaddamar da tantance takardun malaman makaranta a watan Afirilu na wannan shekara.
Alhaji Tijjani Abdullahi ya ce manufar aikin ita ce, a tabbatar da cewa duk wanda yake koyarwa a jihar, yana da takardun da ake bukata kafin ya ci gaba da aiki.
Ya bayyana cewa, hukumar ta tantance takardu 451 ta hanyar tuntubar makarantun da suka bayar da takardun, inda aka samu makarantu 13 sun amsa bukatar da aka tura musu.
Ya kara da cewa, sakamakon da aka samu daga makarantun ya nuna cewa malaman makaranta 233 sun gabatar da takardun bogi wajen daukarsu aiki.
Wannan ya nuna cewa sama da rabin malamai 451 da aka bincika sun gabatar da takardun bogi ne.
Makaranta daya cikin makarantun da aka tuntuba sun musa cewa su suka bayar da takardu ga malamai 212.
Alhaji Tijjani ya kuma ce, za a kori malamai 233 wadanda aka kama da takardun bogin, sannan kuma za a mika fayilansu ga Hukumar Shari’a ta jihar Kaduna domin a yanke musu hukunci.
Ya kara da cewa Hukumar Ilimi Matakin Farko ta jihar za ta cigaba da bincikar ingancin takardun da malaman makarantar suka gabatar yayin daukarsu aiki.