Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa, Customs, ta bude damar neman aiki a hukumar a yau Litinin 13-12-2021.
Hukumar ta fara da bayar da dama ga masu karatun digiri na farko ko babbar diploma da su nemi aikin a matsayin Superintendent Cadre ASC II (CONSOL 08).
Hukumar ta sanya ka’idojin cike neman aikin kamar haka:
- Dole ne mai neman ya kasance dan Najeriya
- Kar tsayin me neman ya gaza mita 1.7 ga maza, da kuma mita 1.6 ga mata.
- Mai neman ya kasance yana da fadin kirjin da bai kasa da mita 0.89 ba.
- Ya kasance yana da shedar kasancewa lafiyayye a jiki da kwakwalwa daga likitan gwamnati.
- Kar ya zama yana fama da jinya a jikinsa ko a kwakwalwarsa.
- Ya kasance wanda ba ya cikin rikicin kudi da zai zubar masa da mutunci.
- Ya zama mai kyakkyawan hali kuma wanda ba a kama da aikata laifi ba a kotu.
- Ya kuma kasance wanda ya iya amfani da na’ura mai kwakwalwa.
- Ya kasance yana da shedar kasancewa dan karamar hukumarsu wadda shugaban karamar hukumar ya sanyawa hannu.
- Mai neman kuma kar ya haura shekaru 30 a duniya.
Hukumar ta kuma yi gargadi na musamman ga masu amfani da takardun bogi, kan cewa ba za ta lamunci hakan ba.
Za a bayar da damar ga masu shaidar karatun NCE da Diploma domin neman matsayin Inspector Cadre AIC, (CONSOL 06) ranar Laraba 15 ga watan da muke ciki.
Haka kuma za a bayar da damar ga masu shaidar karatun sikandire domin neman matsayin Assistant Cadre CA, II, III (CONSOL 03, 04) ranar Jumu’a 17 ga watan da muke ciki.
Jaridar Jakadiya Press za ta kawo muku ka’idojin da za a sakawa masu shaidar NCE, Diploma da kuma sikandire da zarar an saka su.