For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kakakin Majalissar Matasa Ta Jigawa, Haruna Isah, Yai Alƙawarin Kawo Maganin Matsalolin Matasan Jigawa

A ranar 9 ga watan Satumba, 2024, Rt. Hon. Haruna Isah, sabon Kakakin Majalisar Matasa ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, ya gabatar da jawabi a wurin taron da aka gudanar a Cibiyar Bunƙasa Ƙwararru, MDI, da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya bayyana jin dadinsa da godiyarsa ga dukkan matasa da sauran ƴan Jihar Jigawa bisa zaɓensa a matsayin Kakakin Majalisar Matasan, tare da yin alƙawarin yin aiki tuƙuru don inganta rayuwar matasa da al’ummar jihar baki ɗaya.

Hon. Haruna ya yi alƙawarin cewa Majalisar Matasa za ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan dokoki, manufofi, da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, inda ya ce majalisar za ta shirya tarurrukan ne duk bayan watanni uku domin ƙarawa matasa ilimi kan harkokin gwamnatoci a matakin tarayya, jihohi, da na ƙananan hukumomi.

Sabon kakakin ya bayyana damuwa kan ƙaruwar tsanantar matsalolin tsaro, tsadar mai, da haraji mai tsauri da gwamnati ke karɓa, yana mai cewa waɗannan matsaloli sun shafi al’ummar Jigawa, musamman matasa, kuma dole ne a tashi tsaye don ganin an samu sauyi.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kan matasa wajen fitowa fili su nemi gyara, tare da ƙirƙirar manufofi da suka dace da buƙatun matasa, abin da ya ce, zai taimaka wajen tabbatar da cewa muradun matasa suna da muhimmanci a tsarin yanke hukunci na gwamnatoci.

Haruna ya ce majalisar za ta ci gaba da amfani da kafafen sadarwa, haɗin gwiwa da shugabanni, da kuma fafutuka domin ganin an aiwatar da manufofin da zasu amfanar da matasa, tare da adawa da duk wani tsari da zai cutar da matasan.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo sauƙin matsalolin da ke damun jama’a, musamman a wajen samar da manufofin da za su taimaka wajen rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta a halin yanzu.

Haruna ya roƙi matasa su nisanci mutanen da ke neman amfani da siyasa wajen haifar da rikici, tare da buƙatar samun mu’amalar zaman lafiya da neman mafita tare da manyan shugabanni da ƴan kasuwa.

A ƙarshe, ya tabbatar wa matasa cewa zai yi iya ƙoƙarinsa don ganin an cimma burin inganta rayuwar matasa a jihar, tare da yin alƙawarin ba zai ba su kunya ba.

Ya gode wa dukkan mahalarta taron, musamman wakilai daga ƙananan hukumomi 27 na jihar Jigawa, da ya yi fatan sun samu kyakkyawar komawa gida cikin aminci.

Comments
Loading...