Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta ce, idonta ya kai kan wani bidiyon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello me tayar da hankali wanda a cikinsa yake tunzura magoya bayansa, inda ya yi barazanar konewa da kuma jawo gagarumin tashin hankali a kan ‘yan Najeriya a lokacin babban zaben shekarar 2023.
An rawaito cewa, an jiyo gwamnan yana yin muguwar barazana wadda ake cikinta yake cewa, “Ni da kaina zan kunna wuta a hannuna, duk wanda yake so sai mu yi amfani da ita mu kone su, duk wanda ya tsira kuwa (a cikinsu) ya godewa Allah. . . Duk mai adawa da mu zamu sa shi ko ita ta hadu da babata ta kwanta tare da ita a kabari.”
Jam’iyyar PDP ta ce, wannan muguwar barazana ta Yahaya Bello ta tayar hankalin jama’a ganin cewa akwai gungun makasa da aka samar domin yin ta’addanci a kan ‘yan Najeriya a yayin babban zaben 2023, saboda kawai sun ki salon mulkin All Progressives Congress, APC na cin hanci, yaudara da kuntatawa, abubuwan da suka kara tabbata a siyukan Yahaya Bello a Jihar Kogi.
Da take kafa hujja kan zargin da take, mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, ya yi bayanin cewa a ma’anar da FBI ta bayar, ta’addanci shine “yin amfani da karfi ta hanyar da ba ta dace ba, ko tayar da hankalin mutane ko barnata dukiya domin a ci zarafin gwamnati, ‘yan kasa ko kuma wani bangare da ake da shi, a wajen daukaka siyasa ko wata manufar rayuwa”, wannan kuma shine dalilin da ya sa za a iya kiran maganar Yahaya Bello da aikin ta’addanci.
“Daga katobararsa, ‘yan N ajeriya yanzu sun san wadanda suke shirya kisan da yawa daga cikin ‘yan kasarmu, ciki kuwa har da Shugabar Mata ta PDP a Jihar Kogi, Mrs. Salome Abu, wadda aka koneta da ranta a gidanta a shekarar 2019.
“Haka kuma, ‘yan Najeriya yanzu sun samu masaniyar yanda Shugaban PDP na Karamar Hukumar Okene, Adelabu Musa ya bace yau sama da shekaru uku kenan.
“Dadin-dadawa, PDP ta tuna yanda Gwamnatin Kogi karkashin Bello ta shiga cikin zargi na samarwa tare da bayar da makamai ga batagari da kuma jami’an tsaro na karya domin su ci zarafi tare da kai hari kan ‘yan Najeriya a Kogi a lokacin babban zaben 2019.
“Wannan barazana ta tayar da hankalin ‘yan Najeriya, musamman a wannan lokaci, tana da karfin iya kara hargitsa zaman lafiyar al’umma, ta jawo matsala ga shirye-shiryen zaben 2023 ta kuma rusa mana demokaradiyya,” in ji mai magana da yawun PDP.
Saboda haka, PDP ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta dawo da Yahaya Bello kan hanya, sannan ya sanya shi da magoya bayansa cikin wadanda ake kula da su domin tsoron tayar da fitina a matsayin masu barazana ga demokaradiyya a yayin zaben 2023.
Haka kuma, jam’iyyar ta yi kira ga Babban Sufeton ‘Yansanda da ya gaggauta fara yin kwakkwaran bincike kan aiyukan Gwamna Yahaya Bello da nufin kare faruwar mugun abu, sannan kuma ya gurfanar da shi a karshen wa’adinsa.
PDP ta kuma karawa ‘yan Najeriya karfin guiwa, musamman ‘yan Jihar Kogi da cewa, kar su sare saboda Yahaya Bello wanda kwanakinsa na mulki ke karewa, sai dai su ci gaba da lura sannan su ci gaba da kasancewa da PDP a kokarin kubutar da kasa daga hannun ‘yan APC da kuma irin su Yahaya Bello idan 2023 ta zo.