For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kalubale Da Samun Ci Gaba A Ƙaramar Hukumar Guri Karkashin Malam Musa Shu’aibu

Daga: Ahmed Ilallah

Guri, wurin zama……., tabbas a wannan lokacin kananan hukumominmu, musamman ma na arewacin Nijeriya ya zame musu dole su kara tunani wajen bunkasa kananan hukumominmu, ba kawai ta hanyoyin karbar haraji ba, harma da kyakkyawan tunani na shugabanci da jagoarar jama’a ta yadda zasu zamanto masu rike kansu da bada gudunmawarsu ga sauran hukumomi.

Karamar Hukumar Guri bama kawai tana cikin kananan hukumomi masu arziki ba, ita ce karamar hukumar da tafi kowace karamar hukuma arziki ta fannin noma da kiwo a fadin Jihar Jigawa, duba da yadda take da arzikin ruwa, filin noma da daji.

Wannan arzikin ne ya sanya lokaci zuwa lokaci akan samu rashin jituwa harma da rigingimu tsakanin manoma da makiyaya, kusan daman irin wannan rigingimu a wurare masu dausayi irin su Guri a kasarnan ba abun mamaki bane, musamman a wannan lokacin da sana’ar noma take bunkasa, wuraren noma suka zamanto abun nema.

Guri a yau ta fito fili kusan ko ina an santa, musamman a wannan lokaci da akasarin mutane suka kau da kai da ma buri a kan tasirin karamar hukuma wajen yaye musu kuka a matsayinta na gwmantin da tafi kusanci da mutane.

Jagorancin Malam Musa Shu’aibu Guri a karamar hukumar Guri da irin aiyukansa, ya sanya mutane mai da hankalinsu a kan kananan hukumomi, yayin da aiyukan da yake gabatarwa a yau ya mai da Guri wata karamar hukuma abin kallo da kuma kwaikwayo.

Samar da zaman lafiya a irin wannan wurare da kuma ribatar arzikin da Allah ya yiwa wannan yankin ta yadda mutane zasu amfana, su bunkasa tattalin arzikinsu, alúmmah musamman ma matasa su sami aiyukan yi, ya zama dole a samu jajirtaccen shugaba, haziki kuma mai hangen nesa da zai iya bijiro da tsare-tsare da zai taimaki alúmmar sa da kuma bunkasa ita kanta karamar hukumar.

Ziyarar awa biyu da muka yi a Guri don sa ido dama kididdigata ta kashin kai, bisa la’akari da abun da ya faru tsakanin manoma da makiyaya, abubuwa da yawa sun faru na ban sha’awa, ta yadda a ka samu saurin samun zaman lafiya da dawowar harkokin jaama’a a fagen noma da kiwo.

Fasalin gudanarwar karamar hukumar Guri ya samu gagarumin canji da cigaba, yanayi na gudanarwar al’umma ya canja, bunkasar arzikin karamar Guri ya karu, musamman ta fuskar kudin shiga.

A yanzu a kwai kyakkyawan tsari na yaki da talauci, musamman ga matasa da mata, hatta dabaru na yakar fatara sun samu tsari mai kyau bisa jagorancin shugaban karamar humumar Guri Malam Musa Shu’aibu.

Yana daga cikin kyawawan manufofi na shugabanci yin tunani da samar da mafita ga al’umma yayin da suke cikin wani yanayi ko kuma suka keto da ga wani yanayi, wadda wannan mafitar zata taimaka wajen dorewar al ‘umma ta bunkasa arzikin su da kuma zaman lafiya.

Tsarin Shugaban karamar humumar Guri na tallafawa mutanen Guri da hanyoyin da zasu rike kansu da sana’oi daban-daban, kuma wannan shiri bai tsaya kawai a kan wasu bangaren na mutane ba, kusan kowa da kowa daga makiyaya, manoma, matasa, dirobobi, mata kowa yana amfana.

Kyakkyawan tunani na tsara irin wanan manufa ta zamanto mai dorewa shine babban abin farin ciki da zaton cewa al’ummar Guri sun sami shugaba mai tunanin mutanen sa.

Wani babban abin sha’awa game da sabon tsarin jagorancin Musa Shuaibu shine, aiyukan ci gaba da ake samu a karamar hukumar Guri, musamman a bangaren lafiya da ilimi wanda suka hada sabbin gine-gine, gyaran makarantu da kananan asibitoci sun kawo canji da ci gaba a karamar hukumar.

Da ma abin da ake bukata a wurin shugaba wajen jagorancin al’umma shine kykkyawan tunani a yadda al’umma suke da matsalolin su, sannan shugaba ya bijiro da tsare-tsare da taimakawa ya kuma fitar da al’umma daga matsalolin da suke.

Babban buri da al’umma zasu yi a karamar hukumar guri da ma kewaye shine dorewar irin wannan tunani na ciyar da al’umma gaba.

Daukar Nauyi: Ahmed Ilallah

Comments
Loading...