For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kar Ku Bar ISWAP Ta Girma – Zulum Ga Gwamnatin Tarayya

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gargadi Gwamnatin Tarayya kan sakwasakwanta wajen yaki da ta’addanci, inda ya ce kungiyar Islamic State of West Africa, ISWAP tana cigaba da girma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karbar bayanan hukumomi na sati-sati na yau Alhamis a fadar Shugaban Kasa.

Gwamnan ya ce, wannan kira ne mai muhimmanci ga Gwamnatin Tarayya da kuma Sojojin Najeriya domin cike gibin matsalolin yaki da ta’addanci, a matsayin abu mafi muhimmanci, da kuma bukatar a shigo da masu bayar da gudunmawa daga waje.

Da yake nuna takaicinsa kan karuwar da ‘yan kungiyar ISWAP ke yi a wasu sassa na Borno, gwamnan ya ce akwai matukar bukatar inganta tsarin daukar jami’an tsaro na ma’aikatun tsaro, inba haka ba kuma yakin da ake da ta’addanci a kasar ya samu koma baya.

Comments
Loading...