Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ya yi kira ga masu zaɓe a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo da kar guiwarsu ta sare bisa abun da INEC ta yi a zaɓen da ya gabata, inda ya ce su yi tururuwa su fito ranar Asabara domin kaɗa ƙuri’unsu.
Atiku Abubakar wanda a kwanan nan ya kammala ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabarairu a Kotun Ƙoli, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen na ranar Asabar mai zuwa da su zaɓi ƴan takarar jam’iyyar PDP bisa cancantar da suke da ita sama da ƴan takarar sauran jam’iyyu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ƴan takarar jam’iyyar APC a matsayin ƴan gangan a cikin jihohinsu da wajen jihohinsu, inda yai kira ga mutane da su yi watsi da su.
Atiku ya ce, “Duk da dai akwai jin rashin gamsuwa da rashin yarda da yanda Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta (INEC) ta juya baya kan alƙawuranta na aiwatar da gaskiya a zaɓen da ya gabata, amma wannan gazawar ba ta kai ta zama dalilinmu na watsi da tsarin demokaraɗiyya ba.”