For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kar Ku Bari Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni Su Wulaƙanta Ku – Sarki Sunusi Ga Ƴan Najeriya

Bayan nazarin abubuwan da suke ƙasar nan, Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi II ya ce, ƴan Najeriya na karɓar wulaƙanci da yawa daga ƴan siyasar da suka rena su.

Ya yi kiran ƴan Najeriya da kar su bari shugaban ƙasa ko gwamnoni su rena su a ko wanne irin yanayi.

Sarki Sunusi, wanda ke magana a wani faifan bidiyo da ya zagaya kafafen sa da zumunta, ya kuma shawarci talakawa da kar su bari shugabannin siyasa su wulaƙanta su.

Ya ce, idan har ba ana takawa ƴan siyasa birki kan abubuwan da suke na ba daidai ba, to ƴan Najeriyar da za a samu nan gaba zasu rasa ƙasar da zasu kira ta su.

KARANTA WANNAN: Ba Zata Canja Zani Ba, Gwmantin Tinubu Irin Ta Buhari Ce, Ƴan Najeriya Su Shirya Karɓar Ƙaddara

Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, ne kuma Khalifan Ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya ya ce, mafi yawan ƴan Najeriya ba sa siyasa, amma hakan ba yana nufin su ƙasƙantattu ba ne, inda yake kokawa kan yanda ƴan Najeriya suke cikin tsoro a ƙasarsu.

Ya ƙara da cewar abun da ya kamata dukkan ƴan Najeriya su fahimta shine, don mutum bai shiga siyasa ba, hakan ba yana nufin shi wulaƙantacce ba ne.

Ya ce hanya ɗaya da za a ƙwato ƙasar nan sannan a samawa yara gobe mai kyau, ita ce ko da mutum ba ya siyasa, to dole ya zama mai tuhumar ƴan siyasa kan abubuwan da suke yi.

Ya kuma ce, ba za a taɓa samun nutsuwa a irin wannan yanayin ba, sannan yai kira ga matasa da cewar kar guiwarsu tai sanyi, ya kamata su dage su temaka wajen ganin an bunƙasa Najeriya.

Comments
Loading...