For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Karamar Hukuma A Jigawa Ta Magantu Kan Mutuwara Yara Biyu A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

Karamar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa ta magantu kan mutuwar yara biyu a daya daga sansanin ‘yan gudun hijirarta saboda karancin abinci.

Shugaban Karamar Hukumar, Shehu Sule Udi ne ya bayyana hakan lokacin da yake rarraba gudunmawar magani da sauran kayayyaki ga wadanda ruwa ya raba da muhallansu.

An rawaito cewa, yara biyu sun rasu a sansanin Majiyawa saboda abun da ake zargin matsalar rashin wadataccen abinci ne.

Da yake magantuwa kan rahoton, shugaban wanda shugaban sashin lafiya matakin farko na karamar hukumar, Surajo Muhammad ya wakilta ya ce, yaran guda biyu sun rasu ne saboda kamuwa da zazzabin cizon sauro da kuma kyanda, ba saboda karancin abinci ba.

Ya kara da cewa, karamar hukumar na yin iya bakin kokarinta wajen ganin ta samar da kulawar lafiya ga ‘yan karamar hukumar ciki har da wadanda ruwa ya raba da muhallinsu.

“Mun kuma samar da asibitin tafi da gidanka domin bayar da kulawa ga wadanda suka rasa muhallansu a dalilin ambaliyar ruwa,” in ji.

Comments
Loading...